A 2022 Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince Shirin Kawar da Shara a duniya. / Hoto: AA

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yaba wa mai dakin shugaban kasar Turiyya Emine Erdogan a yunkurinta na kawar da shara don tsaface muhalli a duniya yana mai cewa "wannan hangen-nesa nata yana da matukar muhimmanci".

A saƙon da ya aika mata, Guterres ya gode wa Turkiyya tare da haɗin gwiwar Shirin Kula da Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya da UN-Habitat, yana mai cewa "Ina gode wa mai girma Emine Erdogan, mai ɗakin shugaban Turkiyya bisa jajircewarta wajen ganin an alkinta muhalli," a sakon bidiyon da ta aika kan taron na ranar 30 ga watan Maris kan Ranar Kawar da Shara daga New York.

Mai dakin shugaban ƙasar ta jagoranci shirin kawar da sharar a Turkiyya inda ta taimaka ya zama shiri a faɗin duniya, wanda hakan har ya ja Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shirin a 2022.

A karkashin jagorancin uwargidan shugaban Turkiyya Emine Erdogan, Turkiyya ce ke jagorantar ranar Ranar Kawar da Shara ta Duniya, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

A yau, a daidai lokacin da duniya ke murnar zagayowar Ranar Kawar da Shara ta Duniya a karo na biyu, Turkiyya ce kan gaba wurin kawo sauye-sauye da kuma samar da “duniya koriya kuma mai tsafta,” in ji ma’aikatar a sanarwar da ta fitar a shafin X a ranar Asabar.

Ana buƙatar mutane a faɗin duniya su ɗauki ƙananan matakai waɗanda ke da tasiri wurin ciyar da shirin kawar da sharar gaba ta hanyar cewa “daina amfani da roba sau ɗaya da kuma sake sabuntata,” in ji ma’aikatar.

Jagorancin Turkiyya a wannan tafiyar na bayar da muhimmanci kan mayar da hankalin ƙasar ta fuskar kiyaye muhalli da kuma samar da misalai ga wasu ƙasashen da ke faɗin duniya.

Uwargidan shugaban ƙasar ta jagoranci shirin kawar da sharar a Turkiyya inda ta taimaka ya zama shiri a faɗin duniya, wanda hakan har ya ja Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shirin a 2022.

Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, Shirin Kawar da Shara na Duniya na kwaɗaitarwa domin sarrafa kayayyaki cikin aminci da sake sabunta su.

‘Hayaƙi mai gurɓata muhalli na kashe mutum miliyan bakwai duk shekara’ Uwargidan shugaban kasar Turkiyya ta gabatar da jawabi mai karfi a wajen bikin Ranar Kawar da Shara ta Duniya da aka gudanar a birnin Nairobi na kasar Kenya a ranar Larabar nan, inda ta jaddada bukatar gaggauta daukar matakai na hadin gwiwa don tunkarar kalubalen muhalli da kuma ci gaba da kokarin dorewa.

Emine Erdogan ta nuna damuwa matuƙa kan yadda muhallin duniya ke ciki, inda ta yi gargaɗin cewa koguna na fuskantar barazanar ɓacewa saboda rashin amfani da su ba yadda ya dace ba haka kuma ƙasa a faɗin duniya na fama da bola wadda ke ɗauke da sinadarai.

“Hayaƙi mai gurɓata muhalli na kashe mutum miliyan bakwa duk shekara,” kamar yadda ta bayyana, inda ta yi nuni da yadda mutane ke mutuwa sakamakon matsalolin muhalli.

TRT World