Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce ƙasar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da dukkan ƙarfin sojanta wajen kawar da maƙiya idan har wani daga cikinsu ya yi amfani da ƙarfin tuwo a kansa, a daidai lokacin da yake bikin zagayowar ranar kafuwar rundunar sojojin ƙasar, in ji kafar yaɗa labaran Koriya.
KCNA ta rawaito shi yana cewa "Idan maƙiya suka yi ƙoƙarin amfani da ƙarfi a kan ƙasarmu, za mu yanke shawarar sauya tarihi ba tare da jinkirin yin amfani da dukkan ƙarfinmu wajen shafe su ba."
Kim ya sake nanata alkawarin cewa ba zai taɓa yin wata sasantawa da Koriya ta Kudu ba, wadda ya ce ita ce maƙiyar ƙasarsa ta farko, kuma ya ce tsarin shirin soja mai karfi ne kaɗai hanyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga Koriya ta Arewa, in ji KCNA.
Kim ya bayyana a wani babban taron jam'iyya mai mulki na ƙarshen shekarar 2023 cewa sake haɗuwa cikin lumana ba zai yiwu ba, kuma ƙasarsa na yin sauye-sauye kan yadda take mu'amala da Koriya ta Kudu, a wani babban sauyi na sake bayyana alaƙarta da Seoul.
Rahoton na KCNA ya ce Kim ya kai ziyarar ne a Ma'aikatar Tsaron tare da "ƴarsa mai daraja," wadda ke nuni da cewa yana tare da 'yarsa Ju Ae, da manazarta ke ganin za ta taka rawar gani a nan gaba a shugabancin ƙasar.
Koriya ta Arewa ta yi bikin tunawa da kafuwar sojojinta a ranar 8 ga watan Fabrairu, kuma a shekarar da ta gabata, ta gudanar da wani gagarumin faretin soji da tsakar dare, wanda ke nuna manyan makamai masu linzami masu cin nisan zango.
Kalaman na Kim sun zo ne bayan da Majalisar Dokokin Koriya ta Arewa ta kaɗa ƙuri'ar soke dokokin hadin gwiwar tattalin arziki da Koriya ta Kudu.
Majalisar ta kuma amince da babbar murya ga wani shiri na soke wata doka ta musamman kan gudanar da ayyukan yawon buɗe ido na Tsaunin Kumgang, wanda a da wata babbar alama ce ta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Koriya.