Sarkin ya rasu yana da shekara 86 da haihuwa. / Hoto: AA

Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah ya rasu a ranar Asabar da safe.

Ministan Harkokin Masarautar Kuwait Mohammad Abdullah Al-Mubarak Al-Sabah ya ce sarkin ya rasu yana da shekara 86 da haihuwa.

A cewarsa, an kai sarkin asibiti da safe sakamakon bukatar gaggawa amma daga baya Allah ya yi masa rasuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kuwait ya ruwaito.

Ya bayyana cewa ko a watan da ya gabata sai da aka kai sarkin asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sheikh Nawaf ya zama yarima mai jiran gado a 2006, bayan dan uwansa Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya nada shi.

Ya zama Sarkin Kuwait bayan rasuwar dan uwan nasa a Satumbar 2020 a lokacin da yake da shekara 91 da haihuwa.

A halin yanzu Sheikh Mishal al-Ahmad al-Sabah mai shekara 83 shi ne yarima mai jiran gado na kasar

AA