Sakatare Janar na MDD ya koka kan rashin zaman Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro

Sakatare Janar na MDD ya koka kan rashin zaman Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro

‘Ta yaya za a amince da matakin hana bai wa Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro?’ in ji Antonio Guterres.
Guterres ya jaddada kiran da ya yi na kai kayan agaji da kuma tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su. / Hoto: AFP 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki Kwamitin Tsaro na Majalisar bisa rashin bai wa Afirka kujerar mamba ta dindindin a cikinsa.

‘Ta yaya za a amince da matakin hana bai wa Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro?’ in ji Antonio Guterres a sakon da ya wallafa a shafin X.

"Dole ne kungiyoyi su yi nazari kan halin da duniya take ciki a yau, ba abin da ya faru ba shekaru 80 da suka wuce. Taron da za a yi a watan Satumba zai bayar da wata dama ta duba batun sauye-sauyen shugabancin duniya da sake kulla alaka bisa gaskiya," a cewarsa.

Guterres ya jaddada kiran da ya yi na kai kayan agaji da kuma tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

"Ba zan yi kasa a gwiwa ba wurin yin kira a tsagaita wuta nan-take da kai kayan agaji da kuma sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da wasu sharudda ba," in ji shi.

Da yake tsokaci kan halin da ake ciki a Gaza wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren Isra'ila, ya ce: "Al'ummar Gaza suna mutuwa sakamakon harin bama-baia da rashin abinci da wuta da kuma rashin hasken lantarki a asibitoci da rashin magunguna."

AA