Putin ya ce babu wanda ya taɓa daƙile su a tarihi kuma babu wanda zai daƙile su a yanzu ko nan gaba. / Hoto: Reuters

Vladimir Putin ya sanar da cewa nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar Rasha – bayan zaɓen da bai fuskanci wata adawa mai ƙarfi ba – ta nuna cewa ƴan ƙasar sun aminta da jagorancinsa.

“Ina so na yi godiya a gare ku baki ɗaya kan goyon baya da amincin da kuka nuna mani,” kamar yadda Putin ya bayyana a ranar Litinin da safe a wani taron manema labarai a hedikwatar yaƙin neman zaɓensa da ke Moscow.

“Ina so na yi godiya ga ƴan ƙasar Rasha... waɗanda suka zo rumfunan zaɓe inda suka kaɗa ƙuri’a,” kamar yadda Putin ya bayyana bayan sakamakon farko ya nuna cewa shi ne ke kan gaba bayan ya samu kashi 87 cikin 100.

A daidai lokacin da yaƙi da Ukraine ya shiga shekara ta uku, ya yi godiya ta musamman “ga sojojinmu.. waɗanda suka cika alƙawari mafi muhimmanci da suka ɗauka wanda shi ne kare jama’ar ƙasa”.

Ba za a tsoratar da mu ko daƙile mu ba

“Ko wane ne ko kuma duk yadda suke so su tsoratar da mu, kuma duk wanda yake so ya daƙile mu ko niyyar mu – babu wanda ya taɓa yin haka a tarihi. Hakan bai yi aiki a yanzu ba kuma ba zai yi a nan gaba ba.” kamar yadda Putin ya bayyana a wani jawabi ta talabijin.

Mutuwar Navalny ‘lamari maras daɗi’

Putin ya kuma bayyana cewa mutuwar tsohon jagoran yan adawa na ƙasar “lamari ne maras daɗi” inda ya ce har an shirya sakinsa ta hanyar musayar fursunoni.

Ya ce, “dangane da Mr. Navalny. Eh, ya rasu. Wannan lamari ne maras daɗi.” Ya ƙara da cewa “kwanaki kaɗan kafin Mr. Navalny ya rasu, wasu daga cikin abokan aiki sun shaida mani cewa... akwai batun musayar fursuna da Navalny inda za a musaya shi da wasu fursunoni da ke ƙasashen Yamma... sai na ce na amince.”

AFP