“ko dai su wargaza kansu da kansu ko kuma a wargaza su,” Kalaman Fidan kan ƙungiyar ta'addanci ta PKK/YPG. / Hoto: AA

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa gwamnatin rikon ƙwaryar Siriya ba za ta ƙulla alaƙa da ƙungiyar ta'adda ta PKK/YPG ba, inda ya ƙara da cewa ofishin jakadancin Turkiyya da ke Damascus babban birnin kasar zai koma bakin aiki a yau Asabar.

Fidan ya shaida wa kafar yada labarai mai zaman kanta ta NTV a ranar Juma'a cewa, a halin yanzu Syria na da "gwamnatin mai cin gashin kanta" da za ta iya ƙwato yankunanta, yana mai cewa wannan gwamnatin ba za ta amince da ikon ƙungiyar ta'addanci ta PKK/YPG ko kuma "wani iko" a ƙasarta ba.

Fidan ya ƙara da cewa, abin da ake fata shi ne a samar da wani tsari a Siriya inda babu ta'addanci, inda ƙungiyoyin ta'addanci kamar PKK/YPG da Daesh ba za su riƙa samun tallafi ba, ba za a riƙa zaluntar 'yan tsiraru ba, sannan a kuma a samu sukunin biyan buƙatun yau da kullun.

A tsawon shekaru 40 na ta'addancin da ta ke yi wa Turkiyya, PKK - wadda Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka sanya a matsayin ƙungiyar ta'addanci - ta yi sanadin mutuwar fiye da mutane 40,000, ciki har da mata da yara da jarirai, da kuma tsofaffi.

Kungiyar YPG reshen PKK ce a ƙasar Siriya, yankin da ƙungiyar ta shafe shekaru tana ƙokarin kafa wani yankin na ta'addanci a kan iyakar Turkiyya.

Babban jami'in diflomasiyyar na Turkiyya ya yi gargaiɗn cewa kada wani ya kuskura ya yi amfani da makaman kare dangi sannan kuma kada wanda ya yi wata barazana ga ƙasashen yankin.

Ya ce kamata ya yi a tabbatar da haɗin kai da daidaito da zaman lafiya a Syria ta hanyar gwamnatin da ta ƙunshi kowa da kowa.

Fidan ya bayyana burin da Turkiyya ke da shi na kawar da ƙungiyar ta'adda ta PKK/YPG inda ya yi gargadin cewa ko dai su wargaza kansu da kansu ko kuma a wargaza su.

Dangane da batun komawar miliyoyin 'yan gudun hijirar Siriya, ya ce adadin 'yan kasar da za su koma gida zai ƙaru yayin da yanayi a kasar mai maƙawaftaka ya inganta.

Dabarun Turkiyya akan YPG

Fidan ya ce, duk da cewa Turkiyya na da wadata da karfin da za ta iya aiwatarwa, amma da farko Turkiyya za ta jira sabuwar gwamnati a Siriya ta aɗuki matakin kawar da barazanar PKK/YPG.

A ɗaya hannun kuma, yayin da ake kawar da ƙungiyar ta'addanci ta YPG, dole ne a kula domin ganin cewa ba a cutar da Ƙurdawan da suke rayuwa a tsoffin garuruwan yankin tsawon shekaru aru-aru ba.

"Wannan kuwa dole ne saboda zaluncin da YPG ke yi wa Larabawa da Ƙurdawa a ko da yaushe a bayyane yake, ana tsare da su ne inda ake matsin lamba da tilasta musu," in ji shi.

Fidan ya ce, a matakin farko, duk mayaƙan ta'addanci na ƙasa da ƙasa da ba na Syria ba, da ke cikin 'yan ta'addar YPG/PKK, su fice daga ƙasar cikin gaggawa.

A kashi na biyu kuma, ya jaddada cewa, ya kamata dukkan tsarin kwamandojin na YPG, ciki har da 'yan Syria, su fice.

Bugu da kari, ya ce ya kamata 'yan bindigar da ba 'yan ta'addar PKK ba su kwance ɗamara, su shiga cikin tsarin sabuwar gwamnati cikin lumana, su koma ga rayuwar farar hula ta al'ada a Siriya.

An faɗa wa Rasha da Iran kada su sa hannu ta hanyar soji

Fidan ya ce ƙasarsa ta buƙaci kasashen Rasha da Iran da kada su shiga lamarin ta hanyar soji domin tallafa wa Bashar al Assad yayin da mayaƙan da ke adawa da gwamnatin ƙasar suka durfafi Damascus, abin da ya kawo ƙarshen mulkin da Assad da kuma tashin jirginsa zuwa Moscow.

"Abu mafi mahimmanci shi ne tattauna wa da Rashawa da Iraniyawa don tabbatar da cewa ba su shiga cikin tsarin soja ba. Mun yi taro da (su) kuma sun fahimta," Fidan ya shaida wa gidan talabijin na NTV.

Ya ce ko da a ce Moscow da Teheran, dukkansu manyan ƙawayen Assad tun farkon yaƙin basasa a shekara ta 2011, sun taimaka wa Assad, da duk da haka mayaƙan adawa sai sun yi nasara, amma da lamarin ya fi haka ƙazancewa.

"Ko da Assad ya samu goyon baya, 'yan adawa za su iya samun nasara da azamarsu, amma da an ɗauki lokaci mai tsawo kuma za a iya zubar da jini," in ji shi.

Manufar Türkiye ita ce ta "tattaunawa mai mahimmanci tare da manyan ƙasashen guda biyu don tabbatar da taƙita asarar rayuka," in ji Fidan.

TRT World