Mayaƙan Al Qassam sun ce sun tashi wasu bama-bamai a kusa da inda sojojin Isra'ila suke a Rafah inda suka kashe shida daga cikinsu. / Hoto: Reuters

1517 GMT — Rundunar Al Qassam ta ƙungiyar Hamas ta kashe sojojin Isra'ila a Rafah

Rundunar Qassam ta ƙungiyar Hamas ta ce mayaƙanta sun kashe sojojin Isra'ila da dama, sannan suka jikkata wasu a yayin da suka kai hari kan motocin yaƙinsu a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

A wani saƙo da ta wallafa a Telegram, rundunar ta Qassam ta ce mayaƙanta sun yi nasarar “tashi wani bam a kusa da wasu injiniyoyi sojoji inda suka kashe shida tare da jikkata wasu a kusa da mahaɗar George da ke gabashin Rafah".

A wani saƙon na daban, rundunar Qassam ta ƙara da cewa mayaƙanta sun “kai hari bama-bamai a kan tawagar sojojin Isra'ila da motocinsu a yankin Tal Zorob da ke Tal Sultan a yammacin Rafah".

Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai game da sanarwar da Qassam ta fitar ba.

1109 GMT — Sojojin Isra'ila sun kama ƙarin Falasɗinawa 20 a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila a ranar Asabar sun kama akalla Falasdinawa 20 daga yankunan da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da suka mamaye.

A cewar sanarwar hadin gwiwa da Hukumar Kula da Fursunonin da Kungiyar Fursunonin Falasdinu suka fitar, sabon kamen ya kawo adadin Falasdinawa da sojojin Isra’ila ke tsare tun daga ranar 7 ga Oktobar 2023 zuwa 8,975.

An yi kamen ne a biranen Jenin, Nablus, Qalqilya, Bethlehem, Hebron, da kuma Urushalima.

Sanarwar ta kuma ce, yayin gudanar da kamen, sojojin na Isra'ila sun yi wa Falasdinawan duka da cin zarafi tare da lalata musu gidaje da dukiyoyinsu.

0855 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai sabon hari Rafah da safiyar Asabar

Sojojin Isra’ila sun ƙara kai wasu ƙarin hare-hare a Rafah da ke kudancin Gaza ta hanyar amfani da tankokin yaƙi da makaman atilare a ranar Asabar da safe.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa Isra’ila ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare na tsagaita wuta ta dindindin.

Jim kaɗan bayan Biden ya bayar da sanarwar, sai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙin da take yi har sai ta cimma muradunta, daga ciki har da gamawa da Hamas.

Sai dai a nata ɓangaren, ƙungiyar Hamas ta sanar da cewa a shirye take domin ta yi aiki da tsare-tsaren da ake da su a ƙasa na tsagaita wutar.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters

2330 GMT — Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas ta ce ta yi duba da kyakkyawan fata kan wani daftari da Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar na tsagaita wuta na dindindin a zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Biden ya tsara wasu matakai uku na tsagaita wuta daga Isra'il zuwa Hamas don kawo ƙarshen yaƙi a Gaza, wanda ya kashe fiye da Falasɗinawa 36,000 ya jikkata fiye da 82,000, sannan ya jefa rayuwar jama'a cikin mummunan yanayi.

"Hamas ta tabbatar da shirinta na yin aiki da kyakkyawan fata da kuma zuciya buɗe kan duk wani daftari da zai kai ga tsagaita wuta ta dindindin da kuma janyewar [sojojin Isra'ila] gaba daya daga Zirin Gaza, da sake gina [Gaza] da komawar mutanen da aka fitar wurarensu, tare da musayar fursunoni na gaskiya, idan masu mamaya sun bayyana aniyarsu a fili ta yin aiki da yarjejeniyar," kamar yadda ƙungiyar ta faɗa a cikin wata sanarwa.

2130 GMT —Mayaƙan Houthi sun ƙaddamar da hare-hare a yankin Bahar Maliya, in ji Amurka

Mayaƙan Houthi da ke Yemen sun ƙaddamar da hare-hare na makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a Gaɓar Kogin Aden da yankin Bahar Maliya, a cewar Runduna ta musamman ta CENTCOM da ke ƙarƙashin ma'aikatar tsaron Amurka.

"Mayaƙan Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun ƙaddamar da hari da jirgi mara matuƙi a yankunan da ke ƙarƙashin ikonsu na Yemen zuwa yankin Bahar Maliya da misalin ƙarfe 1 da rabi na dare a agogon Sanaa ranar 31 ga watan May," in ji CENTCOM a sanarwar da ta fitar ranar Juma'a.

Sai dai sanarwar ta ce jirgin ya faɗa Bahar Maliya ba tare da jikkata kowa ba.

A wata sanarwar ta daban, CENTCOM ta ce dakarunta sun yi "nasarar" lalata wani jirgi mara matuƙi a Gabar Kogin Aden da kuma wasu jirage uku marasa matuƙa a yankin Bahar Maliya.

Ta ƙara da cewa mayaƙan Houthi sun kai wani hari kuma da makamai masu linzami a Gabar Kogin Aden, ko da yake shi ma bai jikkata kowa ba.

Sai dai sanarwar ta ce jirgin ya faɗa Bahar Maliya ba tare da jikkata kowa ba.. / Hoto: Reuters
TRT World