Yaƙi ya ɓarke a Sudan tun tsakiyar watan Aprilu na 2023. / Hoto:AFP

Ofishin Jakandancin Rasha a Sudan yana bincike kan rahotannin da ke cewa mai yuwuwa an harbo wani jirgi ɗauke da ma'aikatan jirgi na Rasha a yammacin ƙasar.

Ofishin Jakadancin ya faɗa ranar Litinin cewa, zai iya yiwuwa dakarun RSF sun harbo jirgin. RSF dai ɓangare ɗaya ne da ke yaƙi kan samun iko da Sudan.

Ofishin Jakadancin yana aiki da hukumomin Sudan don tattara ƙarin bayanai da kuma tabbatar da makomar mutanen da suke cikin jirgin.

TRT World