Putin ya yi alkawarin taimakwa wa kasashe shida na Afirka wato Burkina Faso, Mali, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Eritrea, Somalia da Zambia yayin taron kasashen Afirka da Rasha da aka gudanar a birnin Saint Petersburg a watan Yulin da ya gabata.

Burkina Faso ta karbi tan 25,000 na alkama ranar Juma'a wadda shugaban Rasha Vladimir Putin ya bai wa kasar a wani bangare na tallafin da zai bai wa kasashen Afirka shida, a cewar jami'ai.

Putin ya yi alkawarin taimaka wa kasashe shida na Afirka wato Burkina Faso, Mali, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Eritrea, Somalia da Zambia yayin taron kasashen Afirka da Rasha da aka gudanar a birnin Saint Petersburg a watan Yulin da ya gabata.

Ministar jinkai na Burkina Faso Nandy Some Diallo ta ce tallafin alkamar ya nuna kudurin Moscow "na taimaka wa ayyukan hukumomin" Ouagadougou a yunkurin magance rashin tsaron da ke addabar kasar.

"Gwamnatin Burkina Faso tana cike da farin ciki," kamar yadda ta bayyana a wani bikin karbar alkamar, tana mai karawa da cewa matakin zai taimaka wa gajiyayyu da marasa galihu.

Jakadan Rasha a kasar Burkina Faso Alexei Saltykov ya ce tallafin alkamar "babbar alama ce ta shirin shugaban Rasha na ganin ya hada kai da Burkina Faso, daya daga cikin aminanmu a Afirka".

Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso Karamoko Jean Marie Traore ya ce matakin zai taimaka wa kasarsu "wajen bunkasa noman alkama ta yadda za mu rage dogaro da wadda ake shigowa da ita daga kasashen waje".

AFP