1505 GMT — Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kalaman shugaban Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga Gaza da kuma miƙa ikon yankin ga Amurka abu ne mai matukar tayar da hankali kuma zai kara tayar da zaune tsaye a yankin Gabas ta Tsakiya.
0742 GMT –– Ministan Tsaron Isra'ila ya bai wa sojoji umarnin tsara ƙaurar Falasɗinawa daga Gaza
Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz ya ce ya bai wa sojoji umarnin tsara shirin barin Falasdinawa su fice daga Gaza idan suna son ƙaura.
"Na bai wa rundunar soji umarnin tsara wani shiri da zai bai wa duk wani mazaunin Gaza son ficewa da ya fita don zuwa duk ƙasar da take son karɓar su," ya ce.
"Shirin zai haɗa da ba da damar ficewa ta dukkan iyakokin ƙasa da ma wani tsari na musamman na fita ta sama da ta ruwa."
Ya ce ya yi maraba da "tsarin da Trump ya yi, wanda zai ba da damar dimbin jama'a a Gaza su tashi zuwa wurare daban-daban a duniya."
Bai ce komai ba a kan ko watan wata rana Falasɗinawa za su koma Gaza, wadda yaƙin da Isra'ila ta shafe wata 15 tana yi a can ya ɗaiɗaita ta tare da mayar da ita kufai.
Trump ya sha nanata shawarar cewa "a share" Gaza a kuma mayar da al'ummarta zuwa Masar da Jordan.
0512 GMT — Malaysia da Iran sun yi watsi da shirin Amurka na raba Falasɗinawa da Gaza
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi watsi da abin da ta kira shiri mai “tsoratarwa” wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na karɓe iko da Gaza da kuma raba Falasɗinawa “karfi da yaji” da muhallansu.
“Shirin da ake yi na kawar da Gaza da kuma raba Falasɗinawa da muhallansu ala tilas zuwa ƙasashen maƙwabta ana kallonsa a matsayin shirin kashe ƙasar Falasɗinu baki ɗaya, kuma ana Allah wadai da hakan,” kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana.
Ita ma ƙasar Malaysia da kakkausar murya ta yi Allah wadai da Shugaba Trump yake yi na sake wa Falasɗinawan Gaza matsuguni. Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta Malayasia ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar.
0213 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce babu wani laifi a ra'ayin Shugaba Donald Trump na korar Falasdinawa daga yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya bayan da shawarar da shugaban Amurkan ya gabatar ta sha suka a duniya.
"Haƙiƙanin ra'ayin shi ne barin 'yan Gaza da ke son tafiya su bar yankin. Ina nufin, me ye matsalar hakan? Za su iya ficewa, za su iya dawowa, za su iya ƙaura su dawo. Amma dole ne ku sake gina Gaza," in ji Netanyahu a wata hira da Fox News.
Ƙarin bayani 👇
0119 GMT — Isra'ila ta fice daga kwamitin kare hakkin bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan jagorancin Amurka Isra'ila ta sanar da ficewa daga Hukumar Kare Hakkokin Dan’Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) bayan matakin da Amurka ta ɗauka na daina shiga cikin hukumar.
Ministan harkokin wajen ƙasar Gideon Sa'ar ya bayyana cewa, "Isra'ila ta yi maraba da matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka na ƙin shiga kwamitin kare hakkin bil'adama na MDD (UNHRC).
Ya ƙara da cewa, "Isra'ila ta bi sahun Amurka kuma ba za ta shiga cikin hukumar ta UNHRC ba."