An hana daya daga cikin ministocin Isra’ila shiga asibiti don duba majinyata. Kazalika wani mutum da aka kasha ‘yan uwansa ya watsa ruwan gahwa kan mai tsaron lafiyar wani ministan na daban, Haka kuma an bayyana wata minister a matsayin “maci amana” kuma “wawiya” yayin da ta je jaje ga iyalan mutanen da aka kasha ‘yan uwansu.
Harin da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba ya sa Isra’ilawa sun hada kai. Amma ba sa kaunar gwamnati wadda suke gani gazawarta ce ta sa aka soma yakin Gaza.
A yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza da aka mamaye, Firaiministan kasar Benjamin Netanyahu yana fuskantar wulakanci, bayan ya shafe tsawon shekaru yana zan zarensa a fagen siyasa.
Salon gudanar da mulkin Netanyahu ya jawo masa kyama da Allah wadai bayan kisan Isra’ilawa akalla 1,300 saboda gazawarsa ta tabbatar da tsaro.
Wani abu da ya jawo masa bakin-jini shi ne shirinsa da ya danganci tsattsauran ra’ayin addini na yin garambawul ga fannin shari’ar kasar a wannan shekarar, wanda ya haddasa jerin zanga-zanga da ta kai har sojoji na musamman suka ajiye ayyukansu.
Wata fitacciyar jaridar Isra'ila Yedioth Ahronoth, ta wallafa babban labarinta da ke cewa "Bala'in Oktoban 2023" inda ya yi waiwaye kan gazawar gwamnati ta gano kutsen da Masar da Syria suka yi wa kasar a watan Oktoba na 1973, wanda ya tilasta wa firaiminista na wancan lokacin Golda Meir yin murabus.
Wannan murabus din ne ya kawo karshen jami'iyyar Labour ta su Meir.
Amotz Asa-El, wata mai bincike a Cibiyar Shalom Hartman da ke Birnin Kudus, ya yi hasashen cewa shi ma Netanyahu da kuma jam'iyyarsa ta Likud sua dab da fuskantar irin wannan makoma.
"Ba sai an yi bincike ko ba a yi ba, ko kuma an gano mai laifi. Kowanne dan Isra'ila yana ganin firaiminista ne ya jawo wannan bala'i," a cewar Asa-El a hira da kamfanin dillancin labaria na Reuters.
"Dole ya sauka daga kam mulki, tare da duk wani abu da ya assasa."
Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da jaridar Maariv ta gudanar ta gano cewa kashi 21 ne kacal suke so Netanyahu ya ci gaba da zama a kan mulki bayan wannan yaki.
Kashi sittin da shida suna ganin "da babu gara ba dadi", yayin da kashi 13 ba su yanke shawara kan makomarsa ba.
Da za a gudanar da zabe yau, kuri'ar jin ra'ayin jama'ar ta gano cewa jam'iyyar Likud za ta rasa kashi daya bisa uku na kujerun majalisar dokoki yayin da jam'iyyar National Unity ta babban mai hamayya da shi Benny Gantz za ta samu karuwa da kashi daya cikin uku — abin da zai ba ta damar zama jam'iyya mai mulki.
Majalisar ministoci ta gaggawa
Sai dai 'yan Isra'ila ba sa son a kada kuri'a. Suna bukatar aiki ne, kuma yayin da akwai yiwuwar dakarun Isra'ila su kutsa ta kasa cikin Gaza, Gantz, wanda tsohon babban hafsan soji ne, ya ce zai ajiye bambancin siyasar da ke tsakaninsa da Netanyahu kuma zai gana da shi a wani taron ministocinsa na gaggawa.
Yayin da yake ganawa da manyan jami'ai da jakadan kasashen waje, Netanyahu ya takaita ganawa da jama'a.
Ya gana da dangin mutane 200 da aka tsare a Gaza, sai dai an hana daukar hoton ganawar a kyamara a lokacin.
Yayin da ake ci gaba da kiraye-kiraye, matarsa ta kai ziyara ga wani iyalai da suke cikin alhini.
Sai dai har yanzu Netanyahu bai fitar da wata sanarwa ba kan abubuwan da yake yi — duk da cewa babban janar dinsa da ministan tsaronsa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro kan tsaro da ministan harkokin waje da ministan kudi da kuma manyan jami'an leken asiri duka sun yi amannar cewa akwai gazawa kan yadda aka kasa dakile farmakin da Hamas ta kai na ba-zata.