Putin ya ce ba ƙasarsa ce "ta soma yaƙi da Ukraine ba", yana mai ɗora alhakin yaƙin kan ƙasashen Yamma da ke goyon bayan Ukraine. / Hoto: Reuters 

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya caccaki ƙasashen Yamma kan bai wa Ukraine makamai masu cin dogon-zango, yana mai cewa Moscow na iya bai wa sauran ƙasashe makamai domin kai hari kan kamfanoni da sauran kayayyaki na Yammacin duniya.

Putin ya bayyana haka ne ranar Laraba — a hira ta musamman da 'yan jaridar ƙasashen duniya ciki har da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency — bayan ƙasashen Yammacin duniya da dama da suka haɗa da Amurka sun ƙarfafa gwiwar Ukraine domin ta kai hare-hare cikin Rasha, matakin da mahukuntan Moscow suka bayyana a matsayin raguwar-dabara.

"Idan wani yana tunanin cewa abu ne mai yiwuwa a aika irin waɗannan makamai fagen-yaƙi domin kai hari ƙasarmu tare da haifar mana da matsaloli, me ya sa suke tunanin ba mu da damar bayar da irin waɗannan makamai ga wasu yankunan duniya domin su kai hare-hare a kan kamfanoni da sauran abubuwa na (ƙasashen Yamma) da ke waɗancan yankuna," in ji Putin.

"Martanin da za mu mayar zai fi nasu ƙarfi. Za mu yi nazari a kansa," kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Putin ya yi watsi da zargin cewa Rasha ta shirya kai hari kan ƙasashe mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO.

"Babu wata buƙata ta yin hakan. Babu buƙatar hakan," a cewarsa.

Kazalika shugaban Rasha ya gardaɗi ƙasashen Yamma cewa matakin da suka ɗauka na bai wa Ukraine makamai "babban kuskure ne", yana mai cewa za su gane kuskurensu nan ba da jimawa ba.

Shugaba Putin ya caccaki ƙasar Jamus bisa aika wa Ukraine makamai, yana mai cewa a lokacin da kason farko na tankokin yaƙin Jamus suka "isa ƙasar Ukraine, Rasha ta yi matuƙar girgiza" domin kuwa hakan ya tuna mata da Yaƙin Duniya na Biyu.

Ya ƙara da cewa dangantaka tsakanin Rasha da Jamus ta lalace bayan da Jamus ta ce "za ta aika ƙarin makamai masu linzami domin kai hari Rasha."

AFP