Wani jami'in na Israila da shi ma ya nemi a sakaya sunansa yace manufar ziyarar ta Gantz ita ce ƙarfafa dangantaka da Amurka, da neman ƙarin goyon baya ga Israila kan yaƙin da ake yi a Gaza da ƙara matsa lamba wajen neman sakin yan Israila da aka yi garkuwa da su. / Hoto: AP Archieve Hoto

Firaiministan Israila Benjamin Netanyahu ya yi kakkausar suka ga daya daga manyan ministocin majalisarsa ta yaƙi wanda ya je birnin Washington domin tattaunawa da jami’an Amurka, kamar yadda wani jami’in Isra'ila da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana, abin da ke nuna wagegiyar ɓarakar da ake da ita tsakanin shugabannin kasar, a lokacin da aka kusa cika wata biyar da yaƙi a yankin Gaza.

Tafiyar ta Banny Gantz, wani abokin hamayyar siyasa da ya shiga majalisar yaki ta Netanyahu bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun ɓaraka tsakanin Amurka da Netanyahu kan yadda za a sauƙaƙa wa Falasdinawa wahalhalu a yankin Gaza, da kuma yadda makomar Gaza za ta kasance bayan kammala yaƙi.

Wani jami’in Jam’iyyar Likuda ta Netanyahu ya ce an shirya tafiya Grantz ne ba tare da sahalewar shugaban na Israila ba.

Jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce Netanyahu ya yi wata zazzafar tattaunawa da Gantz, inda ya shaida masa cewa kasar tana da firaiminista daya ne kawai.

An shirya cewa Gantz zai gana da Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris a ranar Litinin din nan, da mai bai wa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, ranar Talata kuma zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, kamar yadda jam'iyyar Gantz din National Unity Party ta bayyana.

Wani jami'in na Israila na biyu kuma wanda shi me ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa manufar ziyarar ta Gantz ita ce karfafa dangantaka da Amurka, da neman ƙarin goyon baya ga Israila kan yaƙin da ake yi a Gaza da ƙara matsa lamba wajen neman sakin yan Israila da aka yi garkuwa da su.

A Masar kuma, ana ci gaba da tattaunawa kan yadda za a cimma tsagaita wuta kafin watan azumin Ramadana da za a fara a makon gobe.

Israila ba ta tura wakilai ba, saboda tana jiran amsa daga Hamas kan wasu tambayoyi biyu, kamar yadda wani jami'in na gwamnatin Israila na uku da shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana.

Kafafen yada labaran Israila sun ba da rahoton cewa gwamnati tana jiran ta san wadanne ne daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su suke raye, sannan Falasdinawa fursunoni nawa ne Hamas take so a yi musayarsu da kowane daya.

Duka jami'an Isra'ilan uku sun nemi a sakaya sunansu saboda ba a ba su damar yin magana da kafafan watsa labarai kan rikicin ba.

Amurka ta fara jefa kayan agaji ta sama a yankin Gaza ranar Asabar, bayan an kashe gwamman Falasdinawa da suke rige-rigen karbar abincin agaji da Isra'ila ta tsara a makon jiya.

An fara jefa agaji ta sama ne don kaucewa sarkakiyar dake tattare da kai agaji da ake fuskanta saboda tsauraran matakan da Isra'ila ta dauka, da matsalar rabon kayan, da kuma yaki a Gaza.

Wani jami'in ba da agaji ya ce jefa agajin ta sama ba ya tasiri kamar yadda shigar da agaji da motoci ke yi.

Adawa da matakin Netanyahu

Farin jinin Isra'ila ya ragu tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da kazamin yaki a Gaza, kamar yadda mafi yawancin kuri'o'in jin ra'ayin jama'a suka nuna.

Isra'ilawa da dama sun daura masa alhakin gazawa wajen hana haura kan iyaka da Hamas ta yi a ranar 7 ga Oktoba.

An kashe fiye da Falasdinawa 30,000 tun da aka fara yakin, kusan kashi biyu cikin ukunsu mata ne da ƙananan yara, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa a Gaza ta bayyana.

TRT World