Jiragen yaƙin sojin Pakistan sun kai hare-hare a gidajen jama’a a Afghanistan kafin asuba a larduna biyu ranar Litinin, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Afghanistan Zabihullah Mujahid ya bayyana.
A yayin da yake Allah wadai da harin, Mujahid ya bayyana cewa mutum takwas, daga ciki har da yara uku da mata biyar sun rasa rayukansu sakamakon waɗannan hare-haren da aka kai a kudu maso gabashin Paktika da Khost.
An sanar da harin na keta iyaka da misalin 3:00 na dare, kamar yadda ya bayyana. Mujahid ya bayyana cewa Afghanistan ba za ta “bar kowa ya yi mata kutse a cikin ƙasarta ba” inda ta yi kira ga Pakistan da ta dakatar da “tsare-tsare marasa kyau... da kuma lalata dangantaka tsakanin ƙasashen Musulmi biyu masu makwabtaka.”
A yayin da yake gargaɗi kan cewa irin waɗannan lamura na da mummunan sakamako,” ya bayyana cewa”: Masarautar Musulunci ta Afghanistan ba za ta amince da wani ya cutar da yanayin tsaron wani ba ta hayar amfani da ƙasar Afghanistan.” Sunan Taliban a hukumance shi ne Masarautar Musulunci ta Afghanistan.
Tsare-tsare marasa kyau
Harin ta sama wanda ake zargi ya faɗa kan yankin Laman wanda ke a yankin Pakitka da Pasa Mella da ke Khost.
Harin na zuwa ne bayan an kashe sojojin Pakistan aƙalla bakwai, kisan da ake zargi wasu mayaƙa da ke yankin Mir Ali da ke Arewacin Waziristan.
Islamabad na zargin Afghanistan da gazawa wajen hana tsagerun haramtacciyar ƙungiyar Pakistan Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP), hadaddiyar kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban, daga kai hare-hare a Pakistan kafin su koma Afghanistan domin neman mafaka. Afghanistan ta musanta zargin.