An yi jana'izar Falasdinawa da aka kashe a harin da Isra'ila ta kai, a Deir Al-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza / Photo: Reuters

1422 GMT — Mutum 20 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai wani gida mai ɗauke da Falasdinawa kusan 100 a Gaza

Akalla mutane 20 ne suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wani gida da Falasdinawa kusan 100 ke fakewa a cikinsa a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda majiyoyin lafiya suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence ta bayyana cewa, tawagoginta sun zakulo gawarwaki takwas daga ginin gidan zuri'ar Karaja, tare da ceto wasu da dama daga cikinsu, wadanda mata ne da kananan yara.

Kakakin hukumar Civil Defence Mahmoud Basal ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ginin na ba da mafaka ga mutane da dama da suka rasa matsugunansu.

1411 GMT — Muna aiki don warware taƙaddama a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza — Qatar

Qatar ta ce tana kokarin farfado da tattaunawa tsakanin Isra'ila da Hamas don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙasar Majed al-Ansari ya shaida wa taron manema labarai a birnin Doha cewa, ana ci gaba da yin sulhu tsakanin Isra'ila da bangarorin Falasdinawa a Gaza, kuma muna kokarin tantance shi.

Ya ƙara da cewa "Ba za mu yarda wani ɓangare ya yi amfani da mu ba."

Kakakin ya ce Isra'ila ba ta da taswirar da za ta kawo karshen yakin Gaza. "Muna ci gaba da yin aiki tare da 'yan'uwanmu a yankin da kuma Washington don karya lamurra a tattaunawar da ake yi tsakanin Isra'ila da kungiyoyin Falasdinu a Gaza," in ji al-Ansari.

TRT Afrika da abokan hulda