Kafofin yaɗa labaran ƙasar Rasha sun rawaito cewa wasu ƴan bindiga kusan biyar da suka yi ɓad-da-kama ne suka buɗe wuta da makamai masu sarrafa kansu kan mutanen da ke wani gidan rawa na Crocus City da ke kusa da birnin Moscow, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 115 tare da jikkata sama da 145.
Kafofin yada labarai na Rasha sun ce an aike da ma'aikatan ɗaukar marasa lafiya 50 zuwa wurin a ranar Juma'a.
An nuna bidiyon yadda wuta ke ci a sararin samaniya inda baƙin hayaƙi ke tashi a saman gidan rawan.
Magajin garin Moscow Sergei Sobyanin ya ce "Mummunan bala'i ya faru a cibiyar kasuwanci ta Crocus City a yau."
"Ina mai bayyana baƙin cikina na rashin da aka yi."
Sobyanin ya ce za a bayar da duk taimakon da ya dace ga wadanda suka jikkata sakamakon lamarin.
Kafofin yada labaran kasar Rasha sun ce ƴan sanda da sauran jami'an agajin gaggawa sun isa wurin, kuma har a lokacin akwai wasu mutanen a cikin gidan rawar.
A wani bidiyo da ba a tantance ba da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, an nuna maza ɗauke da makamai masu sarrafa kansu suna ta harbin kan mai-uwa-da-wabi kan mutanen da ke ta kururuwa, ciki har da mata, waɗanda ke turereniya a kasa kusa da ƙofar shiga gidan rawan na "Crocus City Hall".
Wasu bidiyoyin sun nuna adadin mutane kwance babu motsi a cikin jini a wajen zauren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya kasa tantance bidiyon nan da nan.
Wani bidiyo ya nuna maharan suna harbin mutanen da ke cikin gidan rawar.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Rasha ya yi gargadi a farkon wannan watan cewa "masu tsattsauran ra'ayi" na da shirin kai hari a birnin Moscow.
Ta bayar da gargadin sa'o'i da dama bayan da Hukumar Tsaron Tarayyar Rasha (FSB), ta ce ta daƙile wani hari da wani gungun 'yan ta'addar Daesh suka kai a wata majami'a a birnin Moscow.