Kafar yada labarai ta Khabarhub ta rawaito cewa jirgin ya yi kama da wuta ne bayan da ya ƙauce daga kan hanyarsa. / Hoto:AA

Mutane 18 sun mutu bayan da wani jirgin fasinja ya yi hatsari a daidai lokacin da yake koƙarin tashi a Kathmandu sai dai an yi sa'a matuƙinsa ya tsira da ransa, a cewar 'yan sandan babban birnin Nepal.

Jirgin na Saurya Airlines na ɗauke da ma'aikata biyu na jirgin sama da kuma 17 na kamfanin waɗanda suka nufi gudanar da aikin gwaji, kamar yadda Dan Bahadur Karki mai magana da yawun 'yan sandan Nepal ya bayyana a ranar Laraba.

"An ceto matuƙin jirgin kuma ana yana samun kulawa yanzu haka, ba za mu iya tabbatar da yanayin da sauran mutanen da ke cikin jirgin suke ba a yanzu, sai dai da dama daga cikinsu ba su tsira ba,'' in ji shi.

Hotunan haɗarin da ya auku waɗanda sojojin Nepal suka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda jirgin ya rabe biyu kana ya ƙone ƙurmus.

Gomman sojoji ne suka tsaya a gaban tarkacen jirgin yayin da ƙura ta lullube wani ɓangare na jirgin da ke ci gaba da ci da wuta.

A sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce, jirgin ya yi haɗari ne da misalin ƙarfe 11:15 na safe (0530 agogon GMT), inda rundunar ta ƙara da cewa tuni tawagar sojojinta da ke aikin ba da agajin gaggawa suka isa wajen domin kai ɗauki.

Kafar watsa labarai ta Khabarhub ta rawaito cewa jirgin ya kama da wuta ne bayan da ya ƙauce daga kan hanyarsa a yayin da yake ƙoƙarin tashi.

An tsara tashin jirgin ne ta hanyar jigilar jiragen sama da aka fi amfani da ita a ƙasar tsakanin Kathmandu da Pokhara, wadda ke zama muhimmiyar cibiyar yawon buɗe ido a jamhuriyar Himalayan.

Kamfanin jiragen sama na Saurya Airlines na jigilar jiragen Bombardier CRJ 200 ne kawai, a cewar shafin intanet na kamfanin.

A shekarun baya bayan nan dai kamfanonin jiragen sama na Nepal suna ƙara bunƙasa, inda suke ɗaukar kayayyaki da mutane tsakanin yankunan da ke da wahalar zuwa da kuma 'yan ƙasashen ƙetare da ke balaguro don hawa kan tsaunuka.

Sai dai ƙasar na fama da matsalar rashin tsaro da aka danganta da rashin samar da isasshen horo da kulawa - waɗanda suka haɗa da manyan tsaunuka da suka mamaye ƙasar.

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta haramta wa duk wani jirgin sama na Nepal shiga sararin samaniyarta saboda rashin tsaro.

Ƙasar tana da hanyoyin jiragen sama masu matukar haɗari a duniya wajen sauka da tashi, tana da tsaunukan dusar ƙanƙara masu tsayi, yanayin da ke zama babban ƙalubale hatta ga ƙwararrun matuƙan jirgi.

Kazalika yanayin tsaunukan na saurin canzawa lamarin da ke iya janyo matsala a yayin tashi da saukar jirgi.

Babban hatsarin jirgin saman fasinjoji na ƙarshe a Nepal shi ne wanda ya auku a watan Janairun 2023, lokacin da wani jirgin saman Yeti ya yi hatsari yayin da yake koƙarin sauka a Pokhana, inda dukka fasinjoji 72 da ke cikinsa suka mutu.

Hatsarin dai shi ne mafi muni da aka taɓa samu tun bayan shekarar 1992, inda gabaki ɗaya mutane 167 da ke cikin jirgin Pakistan International Airlines suka mutu bayan da ya faɗo a kusa da filin jirgin sama na Kathmandu.

A farkon shekarar dai wani jirgin saman Thai Airways ya yi hatsari a kusa da filin jirgin, inda mutane 113 suka mutu.

AFP