Firaminista Hun Manet ya faɗa a shafin Facebook ranar Asabar cewa ya "ji matuƙar kaɗuwa” yayin da ya ji labarin fashewar a sansanin da ke gundumar Kampong Speu.
Ba a iya tantance abin da ya haifar da fashewar makaman ba kai-tsaye.
Hotuna daga inda abin ya faru sun nuna gidajen da suka samu lahani suna cin wuta, da kuma aƙalla gini ɗaya da rufinsa ya faɗi, da kuma sojoji suna samun kulawar likita a wani asibiti.
Wasu hotunan sun nuna wasu gidajen da ramuka a kan rufinsu.
Kanar Youeng Sokhon, wani jami'in soji a wajen, ya ce a wani rahoto taƙaitacce ga shugaban soji Janar Mao Sophan, wanda aka wallafa a soshiyal midiya cewa gine-gine huɗu, uku na adana kaya da guda na yin ayyuka, sun samu lahani yayin da tariin motocin soji suka lalace.
Ya ƙara da cewa gidaje 25 sun lalace a wasu ƙauyuka.
Tsananin zafi
Cambodia, kamar sauran ƙasashen yankin, tana fama da tsananin bujin zafi, inda gundumar da fashewar ta afku ta samu zafi da ya kai digiri 39 a ma'aunin Celsius ranar Asabar.
Yayin da zafin yanayi ba ya haifar da fashewar bama-bamai, amma yana iya raunana ƙarfin makaman na tsawon lokaci, inda zai haifar da haɗarin 'yar ƙaramar fashewa ta janyo jerin fashe-fashe.
Wani shafin labari na Ingilishi, Kiripost ya ambato wani mazaunin kusa da wajen yana cewa, wata babbar fashewa ta faru ne da kusan ƙarfe 2:30 na rana (07:30 GMT), sannan sai ƙananan fashewa suka biyo baya na tsawon awa guda.
An ambato Pheng Kimneang yana cewa tagogin wata masana'anta da ke kusa da wajen sun tarwatse. Sannan gidaje da ke nesa da wajen da kilomita guda (rabin mil) sun samu ƙaramin lahani.
Wasu hotuna sun nuna sansanin da ke wani babban fili, a zahiri ba ya kusa da unguwannin farar hula.
Firaminista Hun Manet ya isar da jajensa ga iyalan sojojin, kuma ya yi alƙawarin gwamnati za ta biya kuɗin jana'izarsu da diyya kan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata.
Hun Manet ya yi karatu a Makarantar Soji ta Amurka da ke West Point. Ya kasance kwamanda a rundunar soji kafin a zaɓe shi bara a matsayin Firaminista, inda ya gaji babansa Hun Sen, wanda ya jagoranci Cambodia tsawon shekaru 38 kafin ya sauka daga mulki.