Salah ya ce hotunan abin da ya faru a asibiti a cikin Gaza da aka yi wa kawanya abu ne “mai tayar da hankali”,/Hoto:Reuters

Shahararren dan wasan Liverpool da kasar Masar Mohamed Salah ya bukaci a bari a gudanar da ayyukan jinkai a yankin Gaza wanda Isra’ila ta yi wa kawanya yayin da ya yi rokon kawo karshen abin da ya kira “kisan kiyashi”.

"Ba abu ba ne mai sauki mutum ya yi magana a irin wannan lokaci. Akwai tashe-tashen hankula da yawa da abubuwa marasa kyau,” in ji Salah kamar yadda ya bayyana a cikin wani bidiyo ga mabiyansa mutum miliyan 62.7 a shafin Instagram.

"Tabarbarewar rikicin a ’yan makonnin nan abu ne mara dadin gani. Kowane rai yana da daraja kuma dole ne a kare shi. Wajibi ne a kawo karshen kisan kiyashin, an tarwatsa iyalai.”

"Abin da ya fito fili a yanzu shi ne wajibi a samar da agajin gaggawa zuwa Gaza ba tare da bata lokaci ba. Mutanen suna cikin mayuwacin hali,” in ji Salah.

Salah ya ce hotunan abin da ya faru a asibitin Al Ahli a cikin Gaza da aka yi wa kawanya suna “tayar da hankali”, kuma Falasdinawa a Gaza suna matukar bukatar abinci da ruwa da magunguna.

"Ina kira ga duniya da su zo su taimaka wajen kare kisan da ake yi wa rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba --- kowa na da damar ya rayuwa.”

TRT Afrika da abokan hulda