Firaministan India Narendra Modi ya shirya ganawa da abokansa na siyasa don tattaunawa kan kafa gwamnati, kwana guda bayan da jam'iyyarsa ta BJP ta rasa rinjaye a majalisar dokoki bayan zaɓen da aka kammala wanda ya bai wa kowa mamaki.
Jam'iyyar BJP ta lashe kujeru 240 a babban zaɓen, ta gaza samun kujeru 32 da za su ba ta rabin yawan kujerun 'yan majalisar dokokin 543 wanda ke bayar da ikon kafa gwamnati ba tare da haɗaka ba, kamar yadda sakamakon zaɓen ya bayyana a yammacin Talatar nan.
Hannayen-jari a kasuwannin hada-hadar jari na NSE Nifty 50 da S&P BSE Sensex a Indiya sun sake faɗuwa da kashi 0.1, bayan tun da farko tun faɗi da kashi shida a ranar Talata, rauni ne da ya haura yadda aka tsammaci nasarar Modi da za ta ƙarfafa gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje.
Rashin ƙarfin ƙawancen da jam'iyyar su Modi ta ƙulla yana iya kawo ƙalubale ga manufofin kaso sauye-sauye na gwamnati, in ji kamfanin da ke auna ƙarfin kasuwar hannun-jari na Fitch
Sai dai kuma, kamfanin ya ƙara da cewa "Duk da rasa rinjaye kaɗan, muna sa ran za a samu ci-gaban manufofin gwamnati da mayar da hankali wajen sauƙaƙa gudanar da kasuwanci da cim ma nasarar harkokin kuɗi a hankali."
Gamayyar jam'iyyun National Democratic Alliance (NDA) wadda BJP ke jagoranta ta lashe kujeru 293, wato tana da ƙarin kujeru 23 kan adadin 272 da ake buƙata don kafa gwamnati, amma Modi a yanzu zai dogara ne kan jam'iyyun yankuna waɗanda ba su da tabbas.
Jaridu na bayyana cewa tauraruwar Modi ta dusashe, inda jaridar Express ta fitar da babban kanunta da ke cewa "India ta bai wa NDA wa'adi na uku, ta aike saƙo ga Modi."
Nasarar da Modi ya samu a kujerarsa ta lardin Varanasi, wajen da ake kallo a matsayin mafi tsarki a tsakanin garuruwan Hindu, ta ragu sosai inda tazarar ba ta haura ta ƙuri'u 150,000 ba, idan aka kwatanta da tazarar ƙuri'u da ya samu a zaɓen 2019.
Amma wannan raguwa ta nasara ba yana nufin sauyi ya samu tasgaro ba ne, in ji shugaban kwamitin kuɗaɗen gwamnati, Arvind Panagariya, a wani rubutu da ya yi a jaridar Economic Times.
Ya ce, "Duk da raguwar adadin kujeru a majalisar dokoki, akwai damar kawo sauye-sauye na tilas. Kawo cigaba mai ɗorewa zai ƙarfafi hannayen gwamnati a shekaru masu zuwa."
Ƙawancen 'yan adawar India da Rahl Gandhi ke jagoranta ya lashe kujeru 230, sama da yadda aka yi hasashe. Jam'iyyar Congress ta Gandhi ta lashe kujeru 99, kusan ninki biyu na kujeru 52 da ta lashe a 2019.