#LOE11 : Israel at war in Gaza after Hamas launches surprise attack / Photo: AFP

1441 GMT — Ministocin Isra'ila sun yi tir da kuɓutar da marayu da dama daga Gaza da aka yi wa ƙawanya

Ministocin Isra'ila biyu sun yi Allah wadai da farmakin da sojojin kasar suka kai na ceto marayun Falasdinawa 70 daga Gaza tare da saukaka tura su zuwa Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye bisa buƙatar Jamus.

Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, ofishin jakadancin Jamus da ke Isra'ila ya bukaci Tel Aviv da ta taimaka wajen miƙa yaran marayu daga yankunan da aka yi wa ƙawanya zuwa Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye.

"Wanda ya tausaya wa azzalumi daga ƙarshe zai zama mai zaluntar masu tausayi," kamar yadda Ministan Kudi Bezalel Smotrich mai tsattsauran ra'ayi ya wallafa a shafin X, yana ambaton wata karin maganar Malaman Yahudu.

"Ina neman ƙarin haske daga Firaiminista game da wane ne ya ba da wannan umarni na rashin tsari kuma a kan wane iko, yayin da ake garkuwa da mutanenmu da ƴaƴansu a can."

Ministan Tsaro na kasa mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir ya kira lamarin da "matakin jinƙai na ƙarya."

0922 GMT — Jirgin ruwa ɗauke da tan 200 na abinci na hanyar zuwa Gaza

Jirgin ruwa ɗauke da kusan tan 200 na abinci ya kama hanyar zuwa Gaza daga wata tashar ruwa ta Kudancin Cyprus, a wani yunƙuri na buɗe wata sabuwar hanya ta ruwa domin kai agaji ga jama’ar Gaza.

Jirgin ruwan na ƙungiyar agaji da ceto ta Open Arms an hange shi yana barin tashar ruwa ta Larnaca ɗauke da kusan tan 200 na shinkafa da fulawa da abincin gina jiki.

Wannan aikin kai agajin, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ke ɗaukar nauyinsa, inda ƙungiyar World Central Kitchen ke shiryawa sai kuma ƙungiyar agaji ta Proactiva Open Arms da ke ƙasar Sifaniya ke bayar da jirgin dakon kayan.

0817 GMT — Maroko ta soma jefa wa jama'ar Gaza kayan agaji ta jirgin sama

Ƙasar Maroko ta shiga sahun wasu ƙasashen duniya domin kai kayan agaji Gaza inda a karon farko ita ma ta jefa wa jama’ar Gaza kayayyakin agaji ta jirgin sama.

Jaridar Hespress ta ruwaito wata majiya daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila tana cewa gwamnatin Rabat ta buƙaci aika jiragen agaji zuwa Tel Aviv da arewacin Gaza.

Gwamnatin ta Morocco tare da haɗin gwiwar Isra’ila sun tura jirage shida ɗauke da kayan agaji.

0604 GMT — Mayaƙan Houthi sun kai wa jirgin ruwan Amurka hari a Bahar Maliya

Mayaƙan Houthi sun kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka Bahar Maliya, kamar yadda mai magana da yawun ƴan Houthin Yahya Sarea ya tabbatar.

“Sojojin ruwan Yemen da taimakon Allah sun kai hari kan wani jirgin Amurka Pinocchio a Bahar Maliya da rokoki na ruwa da dama, kuma an samu jirgin yadda ya kamata, godiya ga Allah,” kamar yadda Sarea ya bayyana a wata sanarwa.

Sarea ya yi gargaɗi kan cewa ƙungiyar za ta ƙara zafafa ayyukan da take yi a cikin watan Ramadana “domin nuna goyon baya ga ƴan uwanmu kuma masu jihadi Falasɗinawa waɗanda ake zalunta.”

Duk da hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Birtaniya ke kai wa mayaƙan, mayaƙan na Houthi na ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan da ke hanyar zuwa Isra’ila ko kuma mallakar Isra’ilar.

2200 GMT — Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen

Amurka da Birtaniya sun kashe aƙalla mutum 11 tare da jikkata 14 a wasu hare-hare da aka kai a yammacin ƙasar Yemen, kamar yadda kakakin gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da shi ya sanar.

An kai hare-hare ta sama aƙalla sau 17 a kasar, ciki har da babban birnin Hudaida mai tashar jiragen ruwa da kuma tashar ruwa ta Ras Issa, a cewar Al Masirah, babbar kafar yaɗa labaran Houthi.

Duk da hare-haren da ƙawancen Amurka da Birtaniya ke kaiwa da kuma na wasu rundunonin sojin ruwa, Houthis sun zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa "mallakar Isra'ila ko mai zuwa Isra'ila" a ɗaya daga cikin manyan hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya.

'Yan Houthi sun ce za a ci gaba da kai hare-hare har sai Isra'ila ta dakatar da mamaye da kuma yaƙi a Gaza.

2151 GMT - Biden ya ce bai shirya ganawa da Netanyahu ba

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce bai shirya ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba.

Biden ya kuma ce ba shi da wani shiri "a halin yanzu" na yin jawabi ga majalisar dokokin Isra'ila.

TRT Afrika da abokan hulda