Kazalika an tattauna kan batun tsaron kasashen Azerbaijan da Armenia, sannan ya nanata cewa nasara kan hakan na da muhimmanci sosai ga yankin. / Hoto: AA Archive

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya buƙaci a gaggauta tsagaita wuta kuma a ƙara yawan ayyukan jinƙai a Gaza.

Ya shigar da buƙatar ce ga wurin Mai Bai wa Shugaban Amurka Shawara kan Tsaro Jake Sullivan yayin wata ganawa a birnin Washington, kamar yadda wasu majiyoyin diflomasiyya suka ruwaito.

Isra’ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 30,000 a Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,200. Rikicin ya sa mutane da dama sun rasa muhallansu da yin asara mai yawa da kuma ƙarancin abinci.

Ganawar ta ranar Alhamis ta ƙara bijiro da batun kada a bari yaƙin Ukraine ya kara yin tsawo, kuma ganawar ta matsa cewa wajibi ne matsayar da za a fitar ta “mutunta iyakoki da makomar siyasar ƙasar Ukraine.”

Kazalika tattaunawar ta taɓo batun yadda Turkiyya take a shirye wajen yaƙi da ƙungiyoyin ’yan ta’adda a Syria, inda ta buƙaci Amurka ta yi aiki da haɗakar kasashe, kuma ta buƙace ta da ta kawo ƙarshen hulƙar da take yi da ƙungiyoyin ƴan ta’adda kamar PKK.

An kuma nuna muhimmancin samun zaman lafiya a Iraqi, inda aka yi magana kan “batun yaƙi da ƙungiyoyin ƴan ta’adda” a yankin.

A ɗaya ɓangaren kuma, Fidan ya gana da Shugaban Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Dattawan Amurka tare da wasu mambobin kwamitin, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayyana.