Meta dai shi ne mallakin manyan shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da Whatsapp./ Hoto: AFP

Katafaren kamfanin fasahar sadarwa Meta ya nemi afuwa kan cire wasu bayanai da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya wallafa kan kisan gillar da aka yi wa shugaban bangaren siyasa na ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh.

A ranar Talata ne kamfanin ya nemi afuwar, kwana guda bayan ofishin Anwar ya gayyaci wakilan Meta don neman ƙarin bayani game da dalilin da ya sa aka cire bayanan da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook da Instagram kan mutuwar Haniyeh.

Meta dai shi ne mallakin manyan shafukan sada zumuntar biyu.

"Muna neman afuwar kuskuren aiki inda aka cire bayanan da ke cikin shafin Facebook da na Instagram ɗin Firaminista," in ji Meta a cikin wata sanarwa da ya fitar.

"Tuni aka dawo da bayanan daidai yadda aka wallafa tare da gasgata alamar tambarin.''

Masu amfani da kafofin intanet na zargin manhajojin Meta da goge bayanai, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasar Hamas.

'Take 'yancin fadin albarkacin baki'

An kashe jagoran siyasar ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a Tehran babban birnin kasar Iran a ranar Laraba a wani hari da aka danganta da Isra'ila.

Bayanan da Anwar ya wallafa sun hada da wani bidiyo da ke nuna Firaministan yayin da yake waya da wani jami'in Hamas yana masa ta'aziyya.

A shafin Instagram, akwai wani saƙo daga Meta da Anwar ya bayyana wanda ya ce an cire bayanan ne saboda alaƙarsa da ''mutane da ƙungiyoyi masu haɗari.''

Ofishin Anwar ya bayyana cire bayanansa da Meta ya yi a matsayin "take 'yancin fadin albarkacin baki ƙarara" tare da neman gafara daga masu fasahar zamani.

A makon da ya gabata ne Anwar ya zargi katafaren kamfanin da “ tsorata” wajen cire bayanansa.

Anwar wanda ya gana da Haniyeh a Qatar a watan Mayu, ya kare alaƙar da ke tsakanin Malaysia da Hamas.

AFP