MDD ta yi kira a gudanar da bincike mai zaman kansa game da harin da Isra'ila ta kai wa ƴan jaridar TRT Arabi

MDD ta yi kira a gudanar da bincike mai zaman kansa game da harin da Isra'ila ta kai wa ƴan jaridar TRT Arabi

Mai ɗaukar hotuna da bidiyo Sami Shehadeh ya yi matuƙar jikkata lamarin da ya kai ga yanke ƙafarsa.
Kazalika wakilin TRT Arabi Sami Berhum da sauran ƴan jaridar da ke tare da shi sun jikkata sakamakon harin./Hoto: AA   

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce harin da Isra'ila ta kai wa tawagar yan jaridar TRT Arabi wani misali ne da ya fito fili ƙarara game da hatsarin da ƴan jarida suke ciki a Gaza,' sannan ta yi kira a gudanar 'bincike mai zaman kansa' kan lamarin.

Ƴan jarida biyu da ke aiki da TRT Arabi sun samu munanan raunuka a sabbin hare-hare da dakarun Isra'ila suka kai ranar Juma'a a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza. Mai ɗaukar hotuna da bidiyo Sami Shehadeh ya yi matuƙar jikkata lamarin da ya kai ga yanke ƙafarsa.

Ganau sun ce dakarun Isra'ila sun kai hari da gangan kan wata tawagar ƴan jarida, cikinsu har da ma'aikatan TRT Arabic, waɗanda ke aiko da rahotanni daga sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat. Wasu ƴan jaridar ma sun jikkata bayan sojojin Isra'ila sun harbe su.

Kazalika wakilin TRT Arabi Sami Berhum da sauran ƴan jaridar da ke tare da shi sun jikkata sakamakon harin.

A cewar Ofishin Watsa Labarai na Gaza, an kashe ƴan jaridar aƙalla 140 tun lokacin da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza.

Rundunar sojojin Isra'ila ta bayar da sanarwa jiya cewa ta kai "harin soji na ba-zata" a tsakiyar Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa da dama.

Darakta Janar na TRT Zahid Sobaci ya yi tur da harin, wanda ya bayyana a matsayin na "ƙeta" da "rashin sanin ya kamata, ba tare da la'akari da dokoki da tsarin jinƙai ba."

TRT World