Sannan irin wannan abu sau biyu yana faruwa a Sweden cikin wata daya da ya wuce . / Photo: AP Archive

Mambobin wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi sun kona Alkur'ani Mai Tsarki a gaban ofisoshin jakadancin Masar da Turkiyya a birnin Copenhagen a ranar Talata, bayan faruwar irin hakan a makonnin da suka wuce a Denmark da Sweden.

Denmark da Sweden sun ce ba sa goyon bayan kona Kur'anin amma sun kasa hanawa saboda bin dokarsu ta bayar da 'yancin fadin albarkacin baki.

Lamarin da ya faru na ranar Talata a Copenhagen da kungiyar masu tsattsauran ra'ayin mai suna "Danish Patriots" ta yi, ya zo ne bayan kaddamar da kona Kur'ani da ta yi a ranar Litinin da kuma makon jiya a gaban ofishin jakadancin Iraki.

Abin da ya jawo a makon da ya gabata masu zanga-zanga a Iraki suka cinna wa ofishin jakadancin Sweden da ke birnin Bagadaza wuta.

Sannan irin wannan abu sau biyu yana faruwa a Sweden cikin wata daya da ya wuce.

A ranar Litinin ne ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta yi kira ga hukumomin kasashen Tarayyar Turai da "su yi gaggawar yin duba kan wannan dokar ta kare 'yancin fadin albarkacin baki" da ake fakewa da shi wajen kona Kur'ani.

A ranar Litinin ma Turkiyya ta yi tur da kakkausar murya kan abin da ta kira "mummunan lamari" da ake yi kan Kur'ani tare da yin kira ga kasar Denmark da ta dauki matakan da suka dace don hana "wannan kiyayya" da ake nuna wa Musulunci.

Gwamnatin kasar Denmark ta yi Allah-wadai da kone-konen Kur'anin tana mai cewa "tsokana ce kuma abin kunya ne" amma ba ta da karfin da za ta hana masu aikata hakan wadanda "ba cikin tashin hankali suke yi ba."

"Mutane kan fake da batun 'yancin albarkacin baki suna aiwatar da abin da suke so," a cewar wani malamin fannin shari'a na Jami'ar Copenhagen, Farfesa Trine Baumbach, a yayin da yake yi wa Reuters bayanin dokokin Denmark.

"Ba kalaman baki kawai dokar ke nufi ba. Mutane na iya yin abin da suke so ta hanyoyi da dama, kamar kona wasu abubuwa da sauran su."

Reuters