Ranar Talata, 3 ga Satumba, 2024
1338 GMT — Masar ta yi watsi da ikirarin Netanyahu na safarar makamai ga Hamas
Masar ta yi watsi da ikirarin da Firaministan Isra'ila Netanyahu ya yi na cewa ana safarar makamai zuwa Hamas ta kan iyakarta.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta kira zargin na Netanyahu da yunkurin kawo cikas ga kokarin shiga tsakani na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma musayar fursunoni.
A ranar Litinin, Netanyahu ya sabunta ƙin amincewarsa ta ficewa daga hanyar Philadelphi, yankin da aka ƙwace daga kan iyakar Masar da Gaza. Firaministan Isra'ilan ya yi ikirarin cewa titin ya kasance "hanyar rayuwa" don Hamas ta sake yin amfani da shi.
Alkahira ta zargi Netanyahu da "kokarin shigar da kasar Masar don karkatar da ra'ayin jama'ar Isra'ila tare da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude da musayar fursunoni, da kuma kawo cikas ga kokarin shiga tsakani na Masar, Qatar, da Amurka."
1021 GMT — Japan za ta yi aiki tare da Falasdinawa don tsagaita wuta a Gaza
Japan ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da Falasdinawa domin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare.
Yayin wata ganawa da shugaban kwamitin Olympics na Falasdinu Jibril Rajoub a birnin Tokyo, Ministan Harkokin Wajen ƙasar Yoko Kamikawa ya bayyana "damuwa sosai" kan halin jinƙai a Gaza.
Ta sake jaddada aniyar kasar Japan na tallafa wa kokarin samar da zaman lafiya da taimakon jinƙai, a cewar wata sanarwa a hukumance.
Ta ƙara da cewa Tokyo na da niyyar "yin aiki kafada da kafada da bangaren Falasdinu don tsagaita wuta," in ji ta.
Ƙarfe 06: 47 GMT - Hare-hare ta sama da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa a faɗin Gaza ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu.
Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya ce an kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani sansani a arewa maso yammacin Khan Younis da ke kudancin Gaza.
A sansanin 'yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Gaza jiragen yakin Isra'ila sun kai farmaki kan wani gida, yayin da motocin sojin Isra'ila suka yi luguden wuta kan sansanin lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka.
0625 GMT — An yi wa yara kusan 159,000 allurar rigakafin cutar shan inna a Gaza: Ma'aikatar Lafiya
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa kusan yara 159,000 ne ake yi wa allurar rigakafin cutar shan inna a yankin tsakiyar Gaza.
"Tawagogin lafiya sun samu damar yi wa yara 158,992 rigakafin a cikin kwana biyu tun bayan fara ta a Gaza," kamar yadda Ma'aikatar lafiyar ta faɗa a wata sanarwar.
Ta ƙara da cewa 'yan ƙasar sun fita sosai don kai yaransu a yi musu allurar rigakafin a rana ta biyu da farawa.
0215 GMT — Biden ya yi amanna Netanyahu ba ya yin abin da ya dace don cim ma yarjejeniyar sakin fursunoni
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba ya tunanin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana yin abin da ya dace wajen kulla yarjejeniya da kungiyar Hamas kan sakin mutanen da ake garkuwa da su.
Kalaman nasa na zuwa a matsayin martani ga tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa a yayin da ya isa Fadar White House.
Biden also said he believes a final deal for the release of hostages held by the Palestinian group is "very close."
Biden ya kuma ce ya yi imanin an kusa cim ma yarjejeniyar karshe ta sakin mutanen da kungiyar Falasdinawan ta yi garkuwa da su."