Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus ya yi magana kan hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza da ta yi wa kawanya.
“A yau karfin Isra’ila bai dogara kan abubuwan da za ta iya yi ba. Abin takaici shi ne babban karfinta ya dogara ne kan yadda za ta raba kan kasashen Musulmai,” kamar yadda ya bayyana a wata hira da jaridar kasar Qatar Al-Sharq a ranar Laraba.
Kurtulmus ya yi magana kan alakar Turkiyya da Qatar da batun harkokin majalisar da harin da Isra’ila take kai wa Gaza da ya saba wa doka da yunkurin gurfanar da Isra’ila a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da matsayar kasashen duniya kan hare-haren da Isra’ila da kuma batun kokarin da Turkiyya take yi kan Falasdinawa ta fuskar diflomasiyya.
Yayin da yake amsa tambayoyi kan alakar Turkiyya da Qatar, ya ce dangantaka ce mai kyau tsakanin kasashen biyu wacce aka gina ta kan ’yan uwantaka.
Ya ce ya yi amanar cewa dangantaka tsakanin Turkiyya da Qatar za ta kasance abin misali ga sauran kasashen yankin.
“Raya wannan dangantaka na da muhimmanci ga duka kasashen biyu. Wannan alaka ta ci gaba da kyautatuwa ta fuskoki da dama,” in ji shi.
Yayin da yake bayyana matsayar majalisar dokokin kasar kan hare-haren Isra’ila kan Gaza, Kurtulmus ya ce sanarwar hadin gwiwa da majalisar ta fitar inda ta yi Allah-wadai da hare-haren Isra’ila ta samu goyon bayan duka bangagorin siyasa da ke majalisar.
Ya ce suna kokarin yin wani tsari na samar da ayyukan jinkai ga Gaza.
Kurtulmus ya ce matsayar majalisar dokokin Turkiyya ta samu amincewar al’ummar kasar kan hare-haren da Isra’ila take kai wa.
“Majalisar Dokokin kasar tana wakiltar al’umma ne,” in ji shi.
Dangane da martanin kasashen duniya kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza, ya nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda aka cika kwana 60 tun bayan fara kai hari Gaza, martanin da kasashen da kungiyoyin Musulmi suke yi ya yi kadan.
“Abin takaicin shi ne mutane suna ci gaba da yin Allah-wadai kan abubuwan da ke faruwa a Gaza cikin bakin ciki, sai dai an kasa daukar kwararan matakai. An kasa daukar matakai don kawo karshen wannan bakar tsanar da dabbanci,” in ji shi.
Kurtulmus ya ce idan ana so a fahimci hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza, to ya kamata a tuna da abubuwan da suka faru kafin hare-haren, ba kawai a fara daga ranar 7 ga watan Oktoba ba.
Ya yi magana kan kalaman tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Condoleezza Rice dangane da sauya iyakokin kasashen Musulmi 22 da abubuwan da ke faruwa a yankin Falasdinawa da Yemen da Lebanon da Syria da Iraki da kuma Libya.