Mai dakin Shugaban Turkiyya ta jagoranci taron Kwamitin Mashawarta na Muhimman Mutane na Majalisar Dinkin Duniya Kan Kawar da Shara karo na uku a Ofishin Shugaban Kasa dake Fadar Dolmabahce a Istanbul.
Ta yi kira da a hada kai a duniya don magance matsalar muhalli da kalubalen kula da shara a yayin da take jawabinta ta bude taron ranar Juma’a.
Emine Erdogan ta bayyana irin kalubalen da matsalar muhalli ke haifarwa, inda ta yi kira ga a dauki matakai na bai daya cikin gaggawa.
“Duk da matsalar da ake fuskanta, za a iya samar da duniya mai cike da adalci,” kamar yadda ta bayyana.
“Za a iya cim ma wannan buri ta hanyar hadin ka. Dukkanmu abokan aiki ne tare a kan wannan fata.
Illoli sakamakon matsaloli na tarihi na da na yanzu
Erdogan ta yi magana game da girman lalacewar muhalli sakamakon matsaloli na tarihi da na yanzu.
Yayin da take ishara da abin da ya biyo bayan yakin duniya na biyu, ta bayyana cewa har yanzu ba a warware wasu illolin da ya haifar ga muhalli ba.
Da ta juya kan rikice-rikice da ake fama da su a yanzu, ta ce, "A yau, kasa daya za ta iya tura bama-bamai daidai da bama-baman nukiliya guda uku a kan wani yanki na farar hula wanda ya kai rabin girman New York," tana nufin hare-haren Isra'ila a Gaza.
Matar ta shugaban Turkiyya ta ce, "Shirin kare muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da rahoton cewa za a iya daukar gomman shekaru kafin a kwashe sharar da ke Gaza. Muna magana ne game da tan miliyan 39 na baraguzai, inda za a iya shafe kusan shekaru 45 kafin a iya sake sarrafa rabinsu."
Ta jaddada cewa dole ne a yi amfani da albarkatu domin gyara duniya, ba don kara lalata ta ba, tana mai jaddada bukatar duniya ta yi gaggawar aiwatar da ayyukan.
Sauyin yanayi
Emine Erdogan ta bayyana mummunan tasirin bala'o'i da suka shafi yanayi, tana mai cewa sama da mutane miliyan 120 ne suka rasa matsugunansu a cikin wannan shekara kadai.
"Yanzu shekaru biyar ne kawai suka rage kafin wa'adin cim ma burin Dorewar Ci Gaban na Sabon Karni na 2030, amma duk da haka muna da sauran tafiya kafin mu cim ma alkawuran da muka yi," in ji ta.