Yawan mutanen da suka fito zaɓen na Ghana ranar 7 ga Disamba a mazaɓu 267 ya kai 60.9%. / Hoto:John Mahama/Facebook

An ayyana tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da yammacin Litinin, bayan da masu kaɗa ƙuri'a suka nuna fushinsu kan yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar tsakanin 2012 zuwa 2017, Mahama, mai shekaru 66, ya samu kuri'u miliyan 6.3, wato kashi 56.5% na ƙuri'un da aka kaɗa, in ji hukumar zaɓen ƙasar.

Babban abokin hamayyar Mahama, Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye a ranar Lahadi. Bawumia ya samu kuri'u miliyan 4.6, wato kashi 41.

Yawan ƙuri’un da aka kaɗa a mazaɓu 267 ya kai kashi 60.9, in ji Shugabar Hukumar Zaɓen Ƙasar Jean Mensa. Mensa ta ƙara da cewa duk da cewa ana ci gaba da ƙidayar ƙuri'u a ɓtara, amma hakan ba zai sauya sakamakon ƙarshe ba.

‘Nasara’ a bayyane

Bayan da Bawumia ya amince da shan kaye a ranar Lahadin da ta gabata, magoya bayan ɗan takarar na hamayya sun gudanar da bukukuwa a sassan ƙasar ciki har da babban birnin ƙasar. Sanye da tufafi masu launin fari, kore, ja da baƙi na jam’iyyar adawa, mata da matasa sun yi ta raye-raye suna kaɗe-kaɗe da busa ƙaho a kan tituna da kuma hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.

An dai gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsadar rayuwa mafi muni a cikin tsararraki.

Ana yi wa zaɓen kallon tamkar wani gwaji ne na dimokuraɗiyya a yankin da tashe-tashen hankula da juyin mulki suka girgiza. Ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka ta ce gaba ɗaya zaɓen ya gudana cikin lumana, wanda ke ci gaba da gudana a Ghana.

Jam'iyyar Mahama ta samu rinjayen kujerun 'yan majalisa

Bawumia dai ya tsaya takarar ne a tutar jam'iyyar New Patriotic Party, ko NPP mai mulki, wacce ta yi ta fama da matsalar tattalin arziki a ƙarƙashin shugaba mai barin gado Nana Akufo-Addo.

Jam'iyyar Mahama ta National Democratic Congress ita ma ta samu rinjaye a majalisar, in ji shi.

Ana kallon nasarar da Mahama ya samu a matsayin sabon salo na zaɓuka a duniya, wanda ke fifita jam'iyyun adawa fiye da masu mulki, daga Amurka zuwa ƙasashen Turai - irin su Birtaniya da Faransa - da kuma Afirka ta Kudu.

‘Nasaba da tattalin arziki'

Kamar dai a yawancin zaɓuɓɓukan da ake yi a Ƙasashen da shugaba mai ci ya sha kaye, ƙuri’un da aka kaɗa a Ghana na nuni da cewa jama’a sun bayyana rashin amincewarsu da gwamnatin da jama’a suka dawo daga rakiyarta, in ji Seidu Alidu, shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa na jami’ar Legon ta Ghana.

"Ina ganin yana da nasaba da tattalin arziki, wanda galibi shi ne batun da ya fi damun kowane ɗan Ghana," in ji Alidu. “Lokacin da mutane suka zaɓe ka, suna buƙatar ka yi musu wasu abubuwa. Sai dai kuma ya shafi salon mulkin ne (saboda) hatta a sauran ƙasashen da ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, gwamnatoci suna fitowa su gaya wa jama’a gaskiya, suna gaya musu haƙiƙanin abin da ke faruwa, da kuma matakan da suka ɗauka wajen tafiyar da shi,” kamar yadda ya bayyana.

TRT Afrika