Mata masu fafutuka sun ce wannan lamari ya fito da yadda mata a India ke ci gaba da shan wahala saboda fyade. / Photo: AA

Dubban ƙananan likitoci a India sun ƙi daina zanga-zangar da suke yi sakamakon fyaɗe da kashe abokiyar aikinsu, inda suka kawo cikas ga ayyukan asibiti kusan tsawon mako guda suna neman a samar da tsaro ga ma'aikatan lafiya da hukunta masu hannu kan lamarin.

Likitoci a faɗin ƙasar sun ci gaba da zanga-zangar inda suka ƙi duba marasa lafiyar da ba sa buƙatar agajin gaggawa, saboda kisan abokiyar aikinsu mai shekara 31 bayan an yi mata fyaɗe a wani asibiti da ke birnin Kolkata na gabashin India.

An kama wani ɗan sandan sa-kai da laifin kisanta tare da tuhumarsa. Mata masu fafutuka sun ce wannan lamari ya fito da yadda mata a India ke ci gaba da shan wahala saboda fyaɗe, duk da tsauraran dokokin da aka samar bayan fyaɗen da aka yi wa wata ɗaliba a 2012 tare da kisanta a cikin motar bas a New Delhi.

Gwamnatin India ta yi kira ga likitoci da su koma bakin aiki sannan ta kafa kwamiti don bayar da shawarwari kan yadda za a bayar da kariya ga ma'aikatan lafiya.

"Za mu ci gaba da ƙauce wa aiki da zaman-dirshan har sai an biya buƙatarmu," in ji Dr. Aniket Mahata, mai magana da yawun ƙananan likitoci a Kwalejin Magani da Asibitin R.G Kar, inda a nan ne lamarin ya faru.

Domin nuna goyon baya ga likitocin, dubban magoya bayan manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa biyu na jihar Bengal ta Yamma sun yi tattaki a titunan Kolkata a yammacin Lahadin da ta gabata suna cewa "Muna so a yi adalci".

Ƙungiyar da ke wakiltar ƙananan likitocin a maƙociyar jihar Odisha, babban birnin New Delhi da jihar Gujarat ta yammacin ƙasar sun ce za su ci gaba da zanga-zangar.

TRT World