1549 GMT — Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai ta yi kakkausar suka kan munanan ayyukan Isra'ila a Gaza
Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai OIC ta yi kakkausar suka kan magoya bayan Isra'ila da suka shafa wa idonsu toka suke mara mata baya da gadara a kan yaƙin da take yi da Gaza, a yayin da Shugaban Amurka Joe Biden ya kai wata ziyarar nuna goyon baya ga Isra'ilan.
Ƙungiyar mai ƙasashe mambobi 57 waɗanda Musulmai ne mafi yawan al'ummarsu sun yi "tir da matsayar ƙasashen duniyar da suke goyon bayan zalincin da ake yi wa Falasɗinawa, da mara wa Isra'ila baya, da kuma yin fuska biyu da ke rufawa Isra'ilan asiri," a cewar sanarwar OIC da aka wallafa jim kaɗan bayan taron gaggawa da ta yi na ministocin ƙasashen wajen mambobinta.
Sanarwar ta zargi Isra'ila da harba rokoki kan Asibitin Al Ahli Arab na Gaza da ya yi sanadin kashe ɗaruruwan mutane a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas.
1731 GMT — Ya kamata Amurka ta goyi bayan binciken kotun ICC idan har ta tabbatar ba Isra'ila ba ce ya kai hari asibitin Gaza: Ƙwararru
Kai harin kan wurare kamar asibitoci "abu ne da aka haramta ɗungurungum" a ƙarƙashin dokar jinƙai ta ƙasa da ƙasa, a cewar wani ƙwararre a fannin shari'a, yana mai jaddada cewa ya kamata kowa ya goyi bayan binciken Kotun Hukunta Miyagun Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa ICC, kan mummunan harin da ya faru a ranar Talata da daddare a kan wani asibiti a Gaza.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Ahmed Abofoul wani mai bincike kan shari'a kuma ma'aikaci a ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Al Haq, ya bayyana cewa kai hari kan asibitoci laifi ne na yaƙi.
Ya ce ba wannan ne karo na farko da Isra'ila ta ƙi ɗaukar alhakin kai hare-hare kan wuraren da fararen hula syuke ba, yana mai ba da misali da harin watan Mayun 2022 da aka kashe wata ƴar jaridar Al Jazeera, Shireen Abu Akleh.
1657 GMT — Shugaban Turkiyya: Kwamitin Tsaro na MDD bai sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ba kan Gaza
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya soki Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya UNSC, kan gazawarsa wajen tabbatar da kudurin da zai ba da damar shigar da kayan agaji zuwa cikin Gaza ta Falasɗinu, a yayin da ake fama da hare-haren da Isra'ila ke kai wa.
Kwamitin Tsaron, "wanda ya zama ba shi da tasiri gaba ɗaya, ya sake gazawa wajen yin aikin da ya rataya a wuyansa," kamar yadda Erdogan ya bayyana a shafinsa na X ranar Laraba, kwana ɗaya bayan da wani harin sama da Isra'ila ta kai kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 500.
"Mummunan harin" da aka kai asibiti ya sa "kisan kiyashin da ake yi a Gaza ... ya shiga wani matakin," a cewar Erdogan, yana mai yin Allah wadai da wadanda suka kai harin "wanda take haƙƙin ɗan'adam ne kuma daidai yake da kisan ƙare dangi a kan al'ummar Gaza."
Shugaban ƙasar Turkiyyan ya kuma yi Allah wadai da Ƙasashen Yamma da kakkausar murya, "waɗanda ba sa barin ko-ta-kwana idan aka zo batun haƙƙoƙin ɗan'adam da ƴancinsa," don ƙin ɗaukar kowane irin mataki na magance wahalhalun da Falasɗinawa suke sha, maimakon haka "sai suke ƙara rura wutar lamarin."
"Waɗanda suka ƙara rura wutar abin da kalamansu da suka yi tun ranar 7 ga watan Oktoba, tamkar su ne suka kai harin kisan kiyashin na jiya tare da wadanda suka kai harin," in ji Erdogan.
Ya kuma sake jan hankula kan "laifukan yaƙin" da Isra'ila ta yi a cikin kwana 12 da suka wuce, yana mai jero harin bama-baman da aka kai kan "mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da suke ƙoƙarin yin ƙaura zuwa wajen da aka ce 'ya fi aminci,' ƙofofin kan iyaka da masallatai da makarantu da kuma wuraren zaman fararen hula."
1521 GMT — Ministan Harkokin Wajen Turkiyya yana ta ƙoƙarin ganin 'an cimma tsagaita wuta ba tare da wasu sharuɗɗa ba' a Gaza
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan yana ta ƙoƙarin ganin "an cimma tsagaita wuta ba tare da wasu sharuɗɗa ba" don dakatar da asarar rayukan da ake yi a Gaza, wacce ke cikin yanayin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda hare-hare da ƙawanyar Isra'ila.
"Abin da ke faruwa a Gaza mummunan take hakin duk wata doka ce ta ƙasa da ƙasa ta haƙƙin ɗan'adam," a cewar Fidan, yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron gaggawa ma Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai OIC a Jiddah.
1850 GMT — Amurka ta hau kujerar na-ƙi a kudurin Kwamitin Tsaro na MDD a kan Gaza
Amurka ta hau kujerar na-ƙi a kan ƙudurin Kwamitin Tsaro na Mjalaisar Dinkin Duniya da ke kira kan a dakatar da rikici tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu don ba da damar shigar da kayayyakin jinƙai da agaji zuwa Zirin Gaza.
Sau biyu ana jan ƙafa wajen kaɗa ƙuri’ar kan ƙudurin da Brazil ta gabatar a kwanakin da suka wuce, a yayin da Amurka ta yi ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar shigar da agaji Gaza.
Mambobin kwamitin 12 sun kada ƙuri'ar amincewa da ƙudurin a ranar Laraba, yayin da Rasha da Birtaniya ƙaurace wa hakan.
Kamar yadda ta saba, Amurka ta bai wa ƙawarta Isra’ila kariya daga duk wani mataki da Kwamitin Tsaro na MDD zai ɗauka a kanta.
A ranar Laraba, Sakatare-Janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a yi gaggawar tsagaita wuta don ba da damar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma shigar da kayan agaji Gaza.
1815 GMT — Mutane da dama sun mutu a wasu hare-haren bam da Isra'ila ta kai wani masallaci a Gaza
Wani harin sama da Isra'ila ta kai kan wani masallaci a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat a yankin tsakiyar Gaza ya hallaka "Falasɗinawa da dama, tare da jikkata wasu," a cewar wata majiyar lafiya.
"Wasu Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da aka kai Masallacin Shaihdai na Al Aqsa," kamar yadda majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu, ba tare da bayyana adadin mutanen da abin ya shafa ba.
Majiyar ta ƙara da cewa an yi ta yin tir da Allah wadai da harin a yankin.
1520 GMT — Firaministan Birtaniya Sunak ya ƙi amincewa da kira a tsagaita wuta
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya ƙi amincewa da kiraye-kirayen da ake yi na tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.
Da yake amsa tambayoyin da mambobin majalisar dokokin ƙasar suke yi masa, Sunak ya ce Isra'ila "na da damar kare kanta, da kare mutanenta da kuma ɗaukar mataki a kan ta'addanci don tabbatar da cewa ba a sake samun irin mummunan harin da Hamas ta kai ba."
Sunak ya ce Isra'ila ta bayyana ƙarara cewa dakarun sojinta za su yi aiki ne bisa tsarin dokokin ƙasa da ƙasa.
"Kuma za su ci ga a da gaya wa Isra'ilawa cewa su ɗauki dukkan matakin da ya dace don kaucewa cutar da fararen huka," Sunak ya faɗa a amsar wata tambaya da shugaban Jam'iyyar Scottish National Party (SNP) Stephen Flynn ya yi masa.
1450 GMT — An kashe Falasɗinawa 12 a harin da Isra'ila ta kai wani gida a kudancin Gaza
An kashe Falasɗinawa 12 a harin saman da Isra'ila ta kai kan wani gida a garin Khan Yunis da ke kudancin Gaza.
Majiyoyin lafiya sun shaida wa Anadolu cewa: "Aƙalla Falasɗinawa 12 aka kashe, gommai suka jikkata a harin da aka kai ya shafi wani gida na zuri'ar Abu Ishaq a gabashin gundumar Khan Yunis.
Harin saman na zuwa ne ƙasa da awa 24 bayan wani harin sama da Isra'ila ta kai kan wani asibiti a Gaza da aka ƙiyasta cewa mutum 500 ne suka mutu a wani lamari da duniya ta yi ta Allah wadai da shi.
1325 GMT — Daruruwan likitocin Pakistan za su kai dauki Gaza
Daruruwan likitoci ‘yan Pakistan sun sadaukar da kansu domin tafiya Gaza bayar da tallafi.
Likitocin sun bukaci kasashen duniya da su kara matsa lamba kan Isra’ila domin ta daina kai hari kan asibitoci da wuraren kiwon lafiya.
Kalubalen da likitocin za su iya fuskanta domin zuwa Gaza shi ne kasar Pakistan ba ta da wata dangataka ta diflomasiyya tsakaninta da Tel Aviv sakamakon ba ta yarda da Isra’ila a matsayin kasa ba.
Sai dai Pakistan kungiyoyin bayar da agajin na Pakistan din na hada kai da takwarorinsu na Turkiyya da Masar domin kaiwa ga Falasdinawa da ke cikin wahala.
1128 GMT — Adadin Falasdinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 3,478, ta jikkata 13,000
Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu ta ce kawo yanzu mutanen da Isra'ila ta kashe a hare-haren da take kai wa Gaza sun kai 3,478, yayin da sama da 13,000 suka jikkata.
Ministar Lafiya ta Falasdinu Mai al Kaila a yayin taron manema labarai a Ramallah,ta ce adadin kiyasi ne kawai saboda mawuyacin halin da ake ciki a Gaza sakamakon ci gaba da hare-haren da Isra'ila take yi.
Ta kuma jaddada cewa ana fama da karancin magunguna a asibitoci a Gaza, haka kuma ta bayyana cewa yawan dauke ruwa da kuma lalacewar magudanan ruwa na kara sa cututtuka suna bazuwa.
1045 GMT — Babu wani uzuri na kai hari kan wani asibiti a Gaza: Shugabar EU
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai ta ce babu wani uzuri na kai hari kan asibiti da ke cike da fararen hula a Gaza.
Ursula von der Leyen ta bayyana haka ne a yayin ganawar da ta yi da yan’ majalisar Tarayyar Turai, inda ta kara da cewa "akwai bukatar a gano gaskiya" kan wannan mummunan harin.
Shugabar ta yi wannan jawabin ne a Strasbourg, tana mai cewa tashin bama-bamai ya afku cikin dare kan asibitin Gaza, inda ya yi sanadin mutuwar mutum 500.
Wannan lamari ya zama tamkar " hukubar wuta". “Dole ne a hukunta duk wadanda suka aikata laifin,” in ji ta, ba tare da ware laifin kai harin ba.
1015 GMT — Likitoci na yin tiyata a kasa ba allurar kashe zafi a Gaza
Likitoci a Gaza wadanda ke fama da karancin kayayyakin aiki na shimfidar da marasa lafiya a kasa tare da yi musu tiyata ba tare da allurar kashe zafi ba, duk a wani yunkuri na ceto rayuwar wadanda Isra'ila ta kai wa hari a asibiti.
Isra’ila ta ci gaba da hare-hare kan Gaza a ranar Laraba, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na Gaza ya bayyana.
Daruruwan Falasdinawa ne suka boye a cikin asibitin Al Ahli da sauran asibitocin da ke Gaza, inda suka nemi mafaka daga hare-hare ta sama daga Isra’ila ke kaiwa, sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
0830 GMT — Halin da ake ciki a Gaza “na neman wuce gona da iri”: WHO
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargadi a kan halin da ake ciki a Gaza bayan harin da Isra'ila ta kai a asibitin Al Ahli wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 500.
"Halin da ake ciki a Gaza na kara kamari," a cewar Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a shafinsa na X.
Ya kara da cewa "muna bukatar kowane bangare ya gaggauta dakatar da wannan rikici. A kowace dakika muna dakon akai agajin gaggawa, muna rasa rayuka. Muna bukatar damar shiga yankin cikin gaggawa don fara isar da kayan ceton rai."
0745 GMT — Rasha na kalubalantar Isra'ila kan ta fito ta wanke kanta kan harin asibitin Gaza
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta kalubalanci Isra’ila kan ta fito da hujjoji wadanda za su nuna ba ta da hannu a kan harin da aka kai asibitin Gaza.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rashar Maria Zakharova ta shaida wa gidan rediyon Sputnik cewa harin babban laifi ne na keta hakkin dan adam.
Ma’aikatar ta ce idan Isra’ila ta san ba ta da hannu a kai harin ta fito da hotunan tauraron dan adam domin wanke kanta.
A halin yanzu Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi kira kan a shirya taron gaggawa na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
0705 GMT — Jordan ta soke taron da za ta yi da Biden bayan Isra'ila ta kai hari asibitin Gaza
Jordan ta soke taron da za ta yi da Shugaban Amurka Joe Biden da shugabannin Masar da Falasdinu inda ta ce “babu amfanin tattaunawa a yanzu kan wani abu sai dai dakatar da yaki.”
Za a gudanar da taron ne “bayan an dauki matakin daina yaki da kuma kawo karshen kisan kare dangin da ake yi,” in ji Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi.
Jordan ta soke wannan taron ne bayan Isra’ila ta tayar da bam a wani asibiti a Gaza, inda sama da Falasdinawa 500 suka mutu, da dama kuma suka samu raunuka.