Wata kotu ta yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a shari'ar da aka fi sani da "cypher case." / Photo: AP Archive

Wata kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaminista Imran Khan daga tuhumar da ake masa da fallasa sirrin gwamnati.

A cikin wani dan takaitaccen hukunci, alkalai biyu na Babbar Kotun Islamabad a ranar Litinin din nan karkashin jagorancin Babban Mai Shari'a Aamer Farooq ya kuma wanke Ministan Harkokin Wajen Khan Shah Mehmood Qureshi, wanda ke da hannu a shari'ar.

Wata kotu ta yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a shari'ar da aka fi sani da "cypher case."

Lamarin dai na da alaƙa da huldar diflomasiyya tsakanin Washington da Islamabad, wanda Khan ya ce wani bangare ne na maƙarƙashiyar da Amurka ta kulla na hambarar da gwamnatinsa shekaru biyu da suka wuce.

Khan, wanda ya hau kan karagar mulki a shekarar 2018, ya rasa kuri'ar amincewa da majalisar dokokin kasar ne a watan Afrilun 2022, shekara daya da cika wa'adinsa.

Duk da wanke shi, Khan zai ci gaba da zama a gidan yari, bayan da kuma aka yanke masa hukunci a wata shari'ar da ta shafi auren matarsa ​​ta uku, Bushra Khan, wanda ya saɓa wa dokokin Musulunci.

TRT World