Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila take kai wa Falasdinawa 'yan jarida da iyalansu a Gaza bayan kisan da ta yi wa iyalan dan jaridar Al Jazeera.
"Mun yi matukar kaduwa game da wani karin cin mutunci da aka yi wa 'yan jarida, inda Isra'ila ta kai hari a gidan dan jaridar Al Jazeera, Wael Al Dahdouh, ta rusa gidansa," kamar yadda Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya bayyana a sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba da daddare.
Altun ya mika ta'aziyyarsa ga Al Dahdouh.
Ya kara da cewa, "Wannan abu ne da muke gani ana yinsa da gangan domin Isra'ila tana kokarin ganin ba a rika bayyana gaskiyar abin da ke faruwa a Gaza ba. Wadannan hare-hare tamkar amfani da ta'addanci ne wajen rufe bakin 'yan jarida."
Hare-haren rashin hankali
Altun ya kara da cewa a yayin da Isra'ila ke ci gaba da amfani da salon tsoratarwa da ta'addanci a kan fararen-hula, a gefe guda wasu jami'an kasar suna sukar Turkiyya kan matsayin da ta dauka na adalci game da hare-haren da ake kai wa a Gaza.
Ya ce, "babu wanda ya isa ya gaya mana abin da ake nufi da ta'addanci. Mun dade muna yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda irin su PKK da Daesh. Babu wani dalili na kai wa fararen-hula hari."
Altun ya ce duniya tana gani ba kawai harin da aka kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba ba, har ma hare-haren kan-mai-uwa-da-wabi da Isra'ila take kai wa fararen-hula a Gaza wadanda suka yi sanadin mutuwar fiye da mutum 6,000 kawo yanzu.
Ya kara da cewa hana kai agaji ga miliyoyin mutanen da aka yi wa kawanye rashin imani da dabbanci ne.