Kim Jong-un ya nemi a karfafa matakan kariya daga hare-hare

Kim Jong-un ya nemi a karfafa matakan kariya daga hare-hare

Kim ya ba da umarnin karfafa daukar matakan kare kasar da gaggawa ta hanyar da ta dace.
Kim ya ba da umarnin karfafa daukar matakan kariya don shirya wa yaki/Hoto (AFP)

Shugaban Koriya ta Arewar Kim Jong-un ya yi kira da a dauki matakan kare kasar daga hare-hare ta hanyar "da ta fi dacewa", kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

Ya nemi daukar matakin ne don a kauce wa abin da ya kira "kutsen" da Amurka da Koriya ta Kudu za su iya yi wa kasar.

Kiran na Kim na zuwa ne a ranar Talata, yayin da kasar ta bude sabuwar shekarar nan da gwaje-gwajen makamai, ciki har da abin da kafar yada labaran kasar ta kira gwajin nukiliya da jirgi marar matuki na karkashin teku, da kuma kaddamar da makamai masu linzami masu cin dogon zango.

A ranar Litinin, Kim ya halarci wani taron Hukumar Koli ta Sojin kasar don tattauna hanyoyin da za a bi "wajen kare kai daga take-taken Amurka da na Koriya ta Kudu na kokarin kaddamar da yaki," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewan ya bayyana.

Kim ya bayar da umarnin karfafa matakan kare kasar daga hare-hare cikin gaggawa kuma ta hanyar da ta dace.

'Yaki na ainihi'

A bara, Koriya ta Arewa ta ayyana kanta a matsayin mai karfin makaman nukiliya, inda take kokarin kawo karshen duk wata tattaunawa don dakile batun nukiliyarta.

A farkon wannan shekarar kuwa, Shugaba Kim ya bai wa rundunar soji umarnin karfafa atisaye don shirya wa "yaki na ainihi".

A wani mataki na mayar da martani, Amurka da Koriya ta Kudu sun karfafa daukar matakan kariya na hadin gwiwa.

Sun fara atisayen soji na hadaka da amfani da manyan jiragen sama na yaki da sauran manyan makamai na Amurka.

Koriya ta Arewa na kallon wadannan jerin atisaye a matsayin gwajin kai mata farmaki, kuma ta bayyana su a matsayin kokarin kaddamar da yaki a kanta.

TRT World