Isra'ila ta ci gaba da killace Gaza tsawon shekaru, tare da mayar da ita 'buɗaɗɗen kurkuku mafi girma a duniya'. / Hoto: AFP

Wani sabon bincike ya gano cewa kashi 64 cikin 100 na Amurkawa suna adawa da shirin Shugaba Donald Trump na mamaye yankin Gaza da aka yi wa ƙwanya tare da sauya shi zuwa abin da ya bayyana da "Riviera of the Middle East."

Mafi yawan waɗanda aka ji ra'ayinsu a binciken sun bayyana matuƙar adawa, inda kashi 47 cikin 100 suka ce "suna matuƙar" adawa da shirin, sai kashi 17 cikin 100 da suka cewa "suna ɗan adawa da shirin", kamar yadda binciken ya nuna, wanda wata cibiyar bincike ta Data for Progress ta bayyana.

Daga cikin 'yan Democrat da aka ji ra'ayinsu, kashi 85 cikin 100 sun yi watsi da ra'ayin, yayin da kashi 43 cikin 100 na Republican ke adawa da shi. A hannu guda kuma, kashi 46 na 'yan Republican sun nuna goyon bayan shirin.

Ƙuri'ar jin ra'ayin, wadda ta yi nazari a kan mutum 1,200 a faɗin Amurka, ta nuna cewa irin wannan shirin zai ƙunshi korar aƙalla Falasɗinawa miliyan 1.8 da a yanzu suke zaune a Gaza zuwa ƙasashe maƙwabta.

"Mafi yawan mutanen suna adawa da Amurka ta samu iko da Gaza da kuma korar al'ummar Falasɗinawa," kamar yadda Data for Progress ta faɗa a cikin bincikenta.

Kisan ƙare dangi na Isra'ila

Shawarar Trump ta korar Falasdinawa, wadda Falasdinawan da sauran kasashen Larabawa da na Musulmai suka yi watsi da ita, na zuwa ne a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a Gaza a ranar 19 ga watan Janairu, ta dakatar da kisan gillar da Isra’ila ke yi na tsawon watanni 15, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 48,200, tare da mayar da yankin kufai.

Isra'ila ta ci gaba da killace Gaza tsawon shekaru, tare da mayar da ita 'buɗaɗɗen kurkuku mafi girma a duniya'.

A lokacin kisan kiyashin da ta yi, Isra'ila ta raba kusan daukacin al'ummar yankin da wajen, lamarin da ya haifar da karancin kayan masarufi da suka hada da abinci, ruwa, magunguna da wutar lantarki.

TRT World