1310 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai hari sansanin gudun hijira inda suka katse wuta da ruwa
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hari sansanonin ‘yan gudun hijira waɗanda ke a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, inda shaidu suka bayyana cewa sojoji sun lalata bututun ruwa da kuma yanke wutar lantarki a wani hari da suka kai kafin asuba.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa wasu mazauna sansanin sun yi ƙoƙarin mayar da martani dangane da harin da sojojin suka kai musu harin.
Sojojin Isra'ila sun kai wasu manya-manyan hare-hare biyu kan sansanin 'yan gudun hijira na Al Fara da ke Tubas a arewa maso yammacin Gabar Yamma da Kogin Jordan, inda suka bar sansanin bayan tsakar dare amma suka dawo cikin sa'o'i biyu da safe, a cewar wata majiya ta Falasdinu.
0716 GMT — Hamas ta yi kira ga Amurka ta matsa lamba ga Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza
Wani babban jami'i a ƙungiyar Hamas ya yi kira ga Amurka ta matsa lamba kan Isra'ila domin ta ƙarshen yaƙin Gaza, gabanin ziyarar da Sakataren Harkokin Wajen Ƙasar Antony Blinken zai kai Gabas ta Tsakiya ranar Litinin don neman tsagaita.
"Muna kira ga gwamnatin Amurka ta matsa lamba kan dakarun mamaya su kawo ƙarshen yaƙin Gaza. A shirye ƙungiyar Hamas take ta amince da duk wani yunƙuri na kirki wanda zai kawo karshen wannan yaƙi," a cewar babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri.
0030 GMT —Netanyahu ya soki Gantz saboda murabus daga gwamnatin gaggawa ta Isra’ila
Firaministan Benjamin Netanyahu ya yi kakkasar suka ga Ministan Majalisar yaƙi Benny Gantz saboda murabus ɗin da ya yi daga gwamnatin gaggawa.
Gantz ya sanar da murabus ɗinsa ne tun da farko a ranar Lahadi, yana ambato muhimman bambance-bambance a yadda ake tafi da al’amura, yana da’awar cewa Netanyahu “ya hana mu cim ma ainihin nasara” a yaƙin da muke a Gaza.
Shi ma wani mai sa ido a majalisar ta yaƙi Gadi Eisenkot, wani tsohon shugaban ma’aikata a rundunar sojan Isra’ila, ya sanar da murabus ɗinsa.
Netanyahu ya faɗa a wani saƙo da ya wallafa a X cewa "Isra'ila na yaƙin ƙoƙarin wanzuwa daga ɓangarori da dama. Bany, yanzu ba lokaci ne na watsi da yaƙin ba, lokaci ne na haɗa ƙarfi waje guda."
“Ƙofata za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga duk ɗan jam’iyyar Yahudawa da ke son ɗaukar wannan nauyi ya kuma taimaka mu yi nasara a kan abokan gabarmu da kuma tabbatar da tsaron 'yan ƙasarmu,” kamar yadda ya bayyana.
Ministan Tsaron Ƙasar mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir ya nemi shiga Majalisar Yaƙin bayan Murabus ɗin Gantz. “Dangane da murabus ɗin Gantz, na miƙa buƙata ga Firaminista ina roƙonsa in shiga Majalisar ta Yaƙi.
Lokaci ne na ɗaukar mataki na jarumta, na samar da tsaro na gaskiya, sannan a samar da tsaro ga Kudu da Arewa da gaɓa ɗayan Isra’ila,” kamar yadda Ben-Gvir ya faɗa a saƙon da ya wallafa a X.
0216 GMT — Hukumar Samar da Abinci ta MDD ta dakatar da aikin agaji a mashigar teku da Amurka ta samar saboda matsalar tsaro
Daraktar Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ta ce ta “dakatar” da raba kayan agaji daga wata mashiga da Amurka ta samar a Zirin Gaza, tana mai cewa “ta damu matuƙa da tsaron mutanenmu,” bayan da aka samu ɗaya daga ranaku mafi muni a yaƙin.
A ranar Asabar ne sojojin Isra’ila suka kai wani hari inda aka kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, amma ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 274 da kuma wani kwamandan Isra’ila guda ɗaya, kuma in ji Cindy McCain, an harba rokoki kan wasu rumbunan WFP guda biyu a Gaza tare da jikkata wani ma’aikaci.
Sanarwar dakatarwar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi, na nuni da koma-baya na baya-bayan nan a hanyar teku ta Amurka ta samar domin kai ƙarin agaji ga mutanen Gaza da ke fama da yunwa.
Hukumar Tallafawa da Ci Gaban Ƙasa-da-Ƙasa ta Amurka USAID ta bayyana dakatarwar a matsayin wani mataki na bai wa ƙungiyoyin agaji damar yin nazari kan tsaro a Gaza.
Hukumar ta USAID tana aiki tare da Hukumar Samar da Abinci ta duniya da takwarorinsu na jin ƙai a Gaza don rarraba abinci da sauran kayan agaji da ke fitowa daga mashigar da Amurka ke kula da ita.
0200 GMT — Amurka ta yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da a kaɗa ƙuri'ar goyon bayan shirin tsagaita wuta a Gaza
Amurka ta sanar a ranar Lahadi cewa ta nemi a kaɗa ƙuri'a a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƙudirinta na goyon bayan "tsagaita wuta nan-take da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su" tsakanin Isra'ila da Hamas.
"A yau, Amurka ta yi kira ga Kwaɗmitin Tsaro ya ɗauki matakin kaɗa ƙuri'a na goyon bayan ƙudrin da aka gabatar," kamar yadda Nate Evans kakakin jakadun Amurka a majlisar ya faɗa, ba tare da ayyana takamaimen ranar kaɗa ƙuri'ar ba