1300 GMT — Akalla karin Falasdinawa 48 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a zirin Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun watan Oktoban bara zuwa 45,484, in ji ma’aikatar lafiya a yankin a ranar Asabar.
A cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar, kimanin mutane 108,090 ne kuma suka jikkata yayin hare-haren kisan kare dangi da ake ci gaba da kaiwa a yankin na Falasɗinawa.
"Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 48 tare da jikkata wasu 52 a kisan kiyashi biyu na iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka wuce," in ji ma'aikatar.
0750 GMT — Akalla Falasdinawa 11 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan fararen hula a arewacin Gaza, da wani gida da ke tsakiyar gabar tekun, da kuma tantunan mutane da ke Khan Younis, inda ake fargabar adadin wadanda suka mutu ya karu.
Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, wani harin da Isra'ila ta kai kan wasu fararen hula a titin Sarari da ke Jabalia a arewacin Gaza, ya kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu da dama.
An kashe karin Falasdinawa tara da suka hada da kananan yara a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan gidan iyalan Naami da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Gaza.
0721 GMT — Isra'ila ta tsare daraktan wani asibiti a Gaza
Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun tsare daraktan wani asibiti a arewacin kasar, wanda hukumar lafiya ta duniya ta ce wani hari da Isra'ila ta kai ya hana shi aiki.
Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar ta ce "Dakarun Isra’ila sun kwashe da yawa daga cikin ma'aikatan lafiya daga asibitin Kamal Adwan zuwa wurin tsare mutane domin yi musu tambayoyi, ciki har da darakta Hossam Abu Safiyeh."
Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta kuma bayar da rahoton cewa, an tsare Abu Safiyeh, inda ta kara da cewa daraktan hukumar a arewacin kasar, Ahmed Hassan al-Kahlout na cikin wadanda ake tsare da su.