Hayaki ya turnuke sararin samaniyar yankin Dahiyeh na Beirut bayan Isra'ila ta kai masa hari. / Hoto: AA

Litinin, 21 ga Oktoba, 2024

2059 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta kai sabbin hare-hare ta sama a Beirut, inda ta fi mayar da hankali a yankunan da ke kudancin wajen babban birnin na Lebanon, bayan Isra'ila ta yi barazanar kai harin bama-bamai kan gine-gine cibiyar harkokin kudi ta Qard al Hassan da ke da alaka da Hezbollah.

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare tara cikin awa daya a kan rassan cibiyar da ke Hayy al Sellum, Borj al Barajneh, da kuma Ghobeiry a kudancin Beirut,a cewar kamfanin dillancin labaran Lebanon na National News Agency.

Tun da farko, rundunar sojin Isra'ila ta yi barazanar kai hari a "muhimmiyar cibiyar harkokin kudi" ta Hezbollah a Lebanon.

Qard al Hassan na daya daga cibiyoyin kudi na Hezbollah, wadda aka kafa a shekarun 1980 domin bayar da sadaka ga al'umma.

0940 GMT — Isra'ila ta kashe mutane 87 a Beit Lahia na Gaza

Adadin mutanen da harin Isra'ila ya kashe a Beit Lahia da ke arewacin Gaza ya kai 87, cewa Ma'aikatar Lafiya a yankin da Isra'ila ta mamaye. Sanarwar ma'aikatar ta ce sama da ƙarin mutum 40 sun raunata, ciki har da waɗanda ke mawuyacin hali.

Tuna bayan 7 ga Oktoban 2023, harin sojojin Isra'ila a Gaza ya halaka aƙalla Falasɗnawa 42,603, kuma ya jikkata 99,795, cewar ma'aikatar.

Wannan adadin bai haɗa da gomman mutanen waɗanda harin cikin daren jiya ya rutsa da su ba, cewar rahoton AFP wanda ya ambato masu ceto.

Isra'ila ta kashe mutane 87 a Beit Lahia na Gaza, adadin kisa ya kai 42,600

1051 GMT — MDD ta yi tir da harin Isra'ila kan Beit Lahiya na Gaza

Jami'in na musamman na majalisar Ɗinkin Duniya Tor Wennesland ya yi tir da harin da Isra'ila ta kai kan garin Beit Lahiya na Gaza, wanda ya kashe gomman mutane, kuma ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-hare kan farar-hula da kare Falasɗinawa da suka tagayyara.

0843 GMT — An kashe ma'aikatan jin-ƙai na Oxfam biyu a harin Isra'ila a arewacin Gaza

Harin Isra'ila na sama ya kashe ma'aikatan ƙungiyar jin-ƙai ta Birtaniya, wato Oxfam biyu a Jabalia ta arewacin, cewar ƙungiyar.

"Oxfam tana jimamin mummunan rashin jami'anmu a Juzoor, Dr Ahmad al Najar da unguwarzoma, Laila Jneid, wannan harin Isra'ila ya kashe a Jabalia,” cewar ƙungiyar jin-ƙan a wata sanarwa a shafin X da yammacin Asabar.

Sanarwar ta ce jami'an biyu suna bayar da muhimmin aikin agaji don ceton rayuka a Gaza.

“Farmaki kan ma'aikatar jin-ƙai lafin yaƙi ne,” in ji Oxfam, inda ta jaddada kiran gaggauta tsagaita wuta a Gaza.

0741 GMT — Isra'ila ta kai harin bama-bamai kan asibitin Kamal Adwan a arewacin Gaza

Asibitin Kamal Adwan Hospital da ke Beit Lahia ya sha ruwan bama-bamai daga hare-haren dakarun Isra'ila, wanda ke ci gaba da luguden bam a arewacin Gaza, cewar wani jami'i a yankin.

Hossam Abu Safiya, daraktan asibitin ya tabbatar cikin wata sanarwa, cewa harin Isra'ila ya lalata tankunan ruwa na asibitin, da babban layin lantarki, wanda ya janyo tsayar da ayyukan kula da lafiya da dama a asibitin.

Ya ƙara da cewa, yankin da ke kewaye da asibitin ya sha matsanancin luguden ruwan bama-bamai da ɓarin wuta tsawon awanni, wanda ya sanya majinyata da jami'an lafiya cikin babban haɗari.

0752 GMT — Sansanin Dakarun zaman lafiya na MDD a kudancin Lebanon ya kunna jiniyar shiga haɗari mataki na 3

An kunna jiniyar da ke nuna shiga haɗari mataki na 3, wanda ke nufin matsanancin haɗari a cikin sansanin sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) a garin Maarakeh, gundumar Tyre a kudancin Lebanon.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon, an yi gargaɗin ne yayin da barazana take da girma a yankin, yayin da ake ci gaba da artabu da faɗan kan iyaka tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyoyin yankin.

Jami'an UNIFIL da mazauna yankin sun shiga cikin barazana babba yayin da yanayin tsaro a kudancin Lebanon yake ci gaba da taɓarɓarewa.

0727 GMT — Sojojin Isra'ila sun yi iƙirarin kai hari kan hedikwatar leƙen asiri ta Hezbollah a Beirut

Isra'ila ta yi iƙirarin cewa sojojinta na sama sun kai farmaki kan hedikwatar leƙen asiri ta Hezbollah, da kuma garejin aiki na ƙarƙashin ƙasa inda suke ƙera makamai a Beirut.

TRT World