Wata kafar watsa labarai ta Amurka MSNBC ta dakatar da wani shiri da ma’aikatanta uku Musulmai ke gabatarwa bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a makon da ya wuce, kamar yadda wasu majiyoyi biyu da abin ya shafa kai tsaye suka sanarwa Arab News.
A ranar Asabar ne Arab News ta rawaito cewa MSNBC ta yanke shawarar ƙin nuna shirin wanda ake sakawa duk mako mai taken 'The Mehdi Hasan Show', sannan kuma ta dakatar da Mohieddine daga gabatar da shirin Joy Reid a ranakun Alhamis da Juma’a.
Majiyoyi sun kuma bayyana wa Arab News cewa za a maye gurbin Velshi da wani mai gabatar da shirye-shiryen da yake gabatarwa a ƙarshen mako.
Sai dai kuma MSNBC ta yi watsi da batun cewa ta nuna wa Hasan ko Mohieddine wariya ta kowace hanya,” kamar yadda wata kafar yada labarai ta intanet ," Semafor ta wallafa a rahotonta.
Amma kuma majiyoyi biyu da abin ya shafa kai tsare sun tabbatar wa da Arab News batun dakatarwar.
“Akwai sarƙaƙiya sosai a kan abind a zai faru a nan gaba,” ɗaya daga ciki majiyoyin ya shaida wa Arab News.
“Amma lamarin ya yi matuƙar kama da abin da ya faru bayan harin 9/11 inda komai yake karkata kan ko dai kana bayanmu ko kuma ba ka tare da mu a wannan gaɓar,” ya ƙara da cewa.
“Abin takaici, a yanzu wannan abin ya wuce batun ra’ayin siyasa ya koma huce haushi kan masu gabatar da shiri da ba a addini ɗaya da su,” ya ce.
Duk da cewa Velshi na ci gaba da bayar da rahotnnin abubuwan da ke faruwa a sauran shirye-shirye, majiyoyin Arab Newssun ce har yanzu ba a san makomar ma’aikatan na MSNBC uku ba.