Biden ya ce babban aikinsa shi ne kare mulkin dimokuradiyya. /Hoto: Biden poll campaign / AP)

Shugaba Joe Biden ya ce zai sake yin takarar shugabancin Amurka don yin wa’adi biyu a fadar White House a shekarar 2024, wani matakin da zai gwada ko Amurkawa za su zabi mai shekara 80, a matsayin shugaban kasa.

Biden, wanda shi ne ya fi shekaru a tarihi a kan karagar mulkin Amurka, ya sanar da aniyarsa ta sake yin takara ne a wani bidiyo yana mai cewa babban aikinsa ne kare dimokuradiyyar Amurka.

Bidiyon ya fara ne da hotuna daga yadda magoya bayan Shugaba Dolad Trump suka auka wa majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2021.

"A lokacin da na nemi shugaban kasa shekaru hudu da suka wuce, na ce muna yakin ceto ran Amurka, kuma har yanzu muna cikin wannan yakin," in ji Biden.

"Wannan ba lokacin da ya kamata mu yi sakaci ba ne. Shi ya sa nake neman a sake zaba ta."

"Bari mu kammala wannan aikin. Na san za mu iya," in ji Shugaba Biden.

Biden ya bayyana jam’iyyar Republican a matsayin barazana ga ‘yancin Amurka, kuma ya yi alkawarin yakar yunkurin takaita kiwo lafiyar mata da rage kudin tallafin tsoffi da gajiyayyu".

Trump ka iya kasancewa abokin hamayyar Biden a jam’iyyar Republican a zaben da za a yi a watan Nuwamban 2024.

A wani martani na gaggawa da jam’iyyar Republican ta fitar kan shelar takarar Mr Biden, ta bayyana shi a matsain wanda bai san halin da ake ciki ba.

"Biden ya sha’afa da ababen da ke faruwa kuma bayan ya haddasa rikici, yana tunanin ya cancanci karin shekaru hudu," in ji wata sanarwa ta kwamitin koli na jam’iyyar Republican.

Ta kara da cewa: "Idan masu zabe suka bari Biden ya ci gaba da shugabanci, farashi zai ci gaba da hauhawa, laifuka za su karu, za a rika shigo da karin miyagun kwayoyi ta kan iyakokinmu da ke bude."

Mafi yawan shekarun da zai nemi mukamin

Cikin shekara biyu bayan ya karbi mulki daga hannun Trump, Biden ya samu amincewar majalisar dokokin kasar kan biliyoyin daloli na gwamnatin tarayya domin dakile annobar korona da gina sabbin ababen more rayuwa.

Ya kuma rage matsalar rashi aiki irin sa na farko tun a 1969, duk da cewar hauhawar farashin kayayyaki da ba a taba gani ba tun shekara 40 da suka wuce ta kawo masa nakasu ta fannin tattalin arziki.

Ba a taba ganin mutum mai shekaru irin na Biden ba da ya sake neman takarar shugabancin Amurka, abin da wasu ke gani a matsayin mataki mai cike da kasada ga jam’iyyar Democratic.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Reuters/Ipsos suka fitar ranar 19 ga watan Afrilu ta nuna cewa wadanda suka amince da Biden ba su wuce kashi 39 cikin 100 ba.

Likitoci sun ayyana Biden, wanda ba ya shan barasa kuma yana motsa jiki sau biyar a mako, a matsayin wada yake "da karfin iya aiki " bayan sun gwada shi a watan Fabrairu.

Fadar White House ta ce bayanan sa sun nuna cewa yana da kaifin basira na fuskantar wahalar aikin.

Kamala Harris, mataimakiyar Biden, za ta kasance abokiyar takararsa a shekarar 2024.

TRT World