Wani jirgin sama-jannatin Amurka da ya samu matsala ya ɓata a wani yanki mai nisa na Kudancin Fasifik, mai yiwuwa ya kama da wuta a sararin samaniya a wani yanayi na gaza cimma nasarar aikinsa na sauka a Duniyar Wata.
An ƙaddamar da jirgin sama-jannatin Peregrine ne a ranar 8 ga watan Janairun nan a ƙarƙashin sabuwar haɗin gwiwa ta gwaji tsakanin NASA da masana'antu masu zaman kansu, da niyyar rage farashi ga masu biyan haraji na Amurka da bunƙasa tattalin arzikin abin da ya shafi Duniyar Wata.
Sai dai jirgin ya fashe jim kaɗan bayan rabuwa da rokar da ke jikinsa, kuma ya riƙa yoyon mai, inda ya lalata harsashinsa na waje, tare da hana kaiwa inda aka nufa.
A cikin sabbin bayanansa, kamfanin Astrobotic ya wallafa a shafin X cewa ya rasa hulɗa da jirgin nasa jim kaɗan kafin ƙarfe 9 na dare agogon GMT a ranar Alhamis, yana nuna "yadda ya sake shiga shiyyar teku" kamar yadda ya yi hasashe.
Kamfanin wanda ke Pittsburgh ya ƙara da cewa zai jira tabbaci mai zaman kansa na makomar Peregrine daga hukumomin gwamnati da abin ya shafa.
Sabuntawar da ta gabata ta samar da daidaitawar sake shiga yanayin sararin duniya daga nisan mil 100 daga kudancin ƙasar Fiji.
Injiniyoyin sun ƙaddamar da wasu ƙananan injuna don su sanya wani mutum-mutumi a kan teku don "rage hadarin yiwuwar tarkacen jirgin faɗawa ƙasa."
Har ila yau Astrobotic a shafinsa na X ya wallafa wani hoton da jirgin ya dauka a ranarsa ta karshe, inda ya nuna yadda jinjirin Wata ya bayyana kansa a tsakanin Rana da duniyarmu.
Peregrine ya yi aiki na tsawon kwanaki 10 a sararin samaniya, inda ya ƙayatar da masu sha'awar harkokin sama-jannati bayan da ya bayyana cewa Astrobotic ba zai yi nasara ba a burinsa na zama kamfani na farko da ya cimma nasara mai sarrafuwa a kan wata - da kuma sauka ta farko lami-lafiya da Amurka za ta yi a Wata tun bayan lokacin Apollo, fiye da shekara 50 da suka wuce.
NASA ta biya kamfanin fiye da dala miliyan 100 a karkashin shirin Commercial Lunar Payload Services (CLPS) don jigilar kayan aikinta na kimiyya zuwa duniyar wata, yayin da take shirin tura 'yan sama-jannatin Amurka komawa zuwa Duniyar Watan a ƴan shekaru masu zuwa a ƙarƙashin shirin Artemis.
Har ila yau, Astrobotic ya ɗauki ƙarin kaya a madadin abokan ciniki masu zaman kansu, kamar DNA da gawarwakin wasu mutum 70, ciki har da na mawallafin Star Trek Gene Roddenberry da marubucin sci-fi Arthur C Clarke.
Ko da yake bai yi nasara ba a wannan karon, jami'an NASA sun bayyana dabarunsu na "akwai damarmaki" na ƙarin damar gwadawa.
Za a ƙaddamar da ƙoƙari na gaba a ƙarƙashin shirin CLPS a cikin Fabrairu.
Jirgin sama-jannatin "Moon Sniper" na Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta kasar Japan da aka harba a watan Satumba, zai kasance jirgi na gaba da zai yi yunkurin sauka a Duniyar Wata a ranar Asabar, wani abu mai matukar wahala.
Idan har ta yi nasara, Japan za ta kasance kasa ta biyar da ta kammala wannan nasara, bayan Tarayyar Soviet da Amurka da China da kuma Indiya.