Jamus ta shiga wani lokaci na rashin tabbas a fagen siyasa ranar Alhamis bayan gwamnatin haɗakarta ta jam'iyyu uku ta wargaje ranar da Donald Trump ya lashe zaɓen Amurka.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz — wanda ya yi shelar gudanar da amintaccen zaɓe a watan Janairu, wanda zaɓen gaggawa zai iya biyo bayansa a watan Maris — zai nemi ya sake bai wa takwarorinsa na Turai tabbaci a wani taro a Budapest.
Ranar Laraba ne Scholz ya ce zai yi bikon shugaban 'yan adawa masu ra'ayin riƙau Friedrich Merz, wanda ke kan gaba a ƙuri'un jin ra'ayin jama'a, don samun goyon baya kan muhimman ƙudurori da suka shafi tattalin arziki da tsaro.
Ƙarshen ƙawancen jam'iyyu uku mai cike da ce-ce-ku-ce, wanda ya hana shi gwamnati mai rinjaye, ya zo ne a wani mawuyacin lokaci a ƙasar mafi ƙarfin tattalin arziki a Turai, wadda ke daf da sake samun raguwar tattalin arziki karo na biyu a jere.
"Wargajewar ƙawancen da wuri ta saka Jamus cikin halin rashin tabbas a wani lokaci da zai iya kasancewa mai hargitsi da yawa bayan Donald Trump ya lashe zaɓe," in ji Holger Schmieding, wani mai sharhi na bankin Berenberg mai zaman kansa .
Amma Schmieding ya ce zaɓen gaggawa da kuma sabon shugabanci a farkon shekarar 2025 za su iya taimakawa tunda "rashin jituwa a ko da yaushe a ƙawancen jam'iyyu ukun ta hana samun ci-gaba".
Scholz ne ke jagorantar taron ƙungiyar Tarayyar Turai a Budapest ranar Alhamis domin tattaunawa kan rikice-rikicen duniya, musamman yaƙin Ukraine da Rasha da kuma rikicin Gabas ta Tsakiya, waɗanda sauyin da ke tafe a fadar White House zai shafa.
Shugabannin ƙungiyar Tarayyar Turai suna haɗuwa domin tattaunawa a inda da mai masauƙin baƙi, Firaministan Hungary Viktor Orban, yake ɗaya daga cikin waɗanda suka fi rashin amincewa da bai wa Kiev tallafi a Ƙungiyar Tarayyar Turai.
'Dabarun siyasa na rashin kara'
Bayan watannin da aka kwashe ana ƙazamin faɗan cikin gida a cikinta, ƙawancen jam'iyyar Social Democrats (SPD) ta Scholz da jam'iiyar Greens da kuma jam'iyyar Free Democrats (FDP) mai taimaka wa kasuwanci ya watse ranar Laraba da daddare.
A wani mataki mai ban mamaki, Scholz ya kori ministan harkokin kuɗinsa mai yawan faɗa, Christian Lindner, lamarin da ya tilasta wa jam'iyyar FDP ficewa daga ƙawancen inda ta bar jam'iyyun SPD da Greens a cikin gwamnati mai rashin rinjaye da cike da rashin tabbas.
Shugaban gwamnatin Jamus ɗin ya ce zai nemi a yi zaɓen amincewa da gwamnati nan da 15 ga watan Janairu don 'yan majalisa su yanke shawara kan ko za su nemi a yi zaɓen gaggawa wanda za a iya yi watanni shida kafin yadda aka shirya yinsa a watan Satumba.
Har zuwa wancan lokacin, gwamnatin ta mara rinjaye za ta iya yin wasu dokoki ne idan ta samu goyon bayan 'yan adawa.
Scholz ya yi wa Lindner kakkausan maganganu ranar Laraba, inda ya ce babu wata "maganar amana" tsakaninsu.
Ya soki korarren ministan kuɗin don "dabarun siyasarsa na rashin kara" tare da zarginsa da kasancewa mai wani matakin son-kai "da ya wuce tunani".
Jam'iyyar FDP, mafi ƙaranci jam'iyya cikin ƙawancen, ta daɗe da samun bambancin ra'ayi da jam'iyyar SPD da Greens kan wasu batutuwa, musamman ta yadda za a tsara kasafin kuɗi da kuma tayar da tatalin arziƙin Jamus mai matsala.
Lindner ya daɗe yana tunanin barin ƙawancen kuma ya yi gargaɗin "kakar yanke shawarwari" yayin da ranar ƙarshe ta tattaunawa kan kasafin kuɗi ke karatowa a mako mai zuwa.
Scholz ya bayyana cewa "a halin yanzu muna buƙatar cikakken bayani game da yadda za mu saka isasshen kuɗi a fannin tsaronmu a cikin shekaru masu zuwa ba tare da yin barazana ga haɗin kan ƙasarmu ba".
"Idan aka yi la'akari da zaɓen Amurka, da alama wannan ya fi buƙatar matakin gaggawa a halin yanzu fiye da a baya."