Shugaban na Hezbollah ya ce goyon bayan na da muhimmanci domin “fito na fito da barazanar da Isra’ila ta kasance a yankin ". / Hoto: AA

Sabon shugaban Hezbollah ya ce ƙungiyarsa ba ta faɗa a madadin Iran, amma domin kare ƙasar Lebanon da 'yantar da ita.

"Mu a Lebanon ba ma yaƙi a madadin Iran ko kuma domin mu aiwatar da shirinta, sai domin kare ƙasarmu da 'yantar da ita," a cewar Naim Qassem a wani jawabi da aka naɗa ranar Laraba. "Mun kwashe watanni 11 muna cewa ba ma son yaƙi, amma a shirye muke idan aka tilasta mana shi."

An naɗa Qassem a matsayin sabon shugaban Hezbollah ranar Talata, inda ya gaji Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a wani harin sama da Isra’ila ta kai Beirut a watan jiya.

"Niyyata ce na ci gaba da salon Nasrallah na kasance a kan hanyar yaƙi bisa ga yadda abubuwa ke wakana," in ji shi. "Gwagwarmayar ta kasance ne domin ‘yanta ƙasarmu da yin fito-na-fito da masu mamaya da kuma niyyarsu ta faɗaɗa mamaya a yankin."

Taimaka wa Gaza

Shugaban na Hezbollah ya ce taimaka wa Gaza ya zama wajibi domin "ƙalubalantar barazanar da Isra’ila ke yi wa Zirin Gaza, kuma mutanen Gaza suna da ‘yanci a matsayinsu na mutane da Larabawa da Musulmai da kuma na ‘yan ƙasa na dukkanmu mu mara musu baya ".

"Wannan yaƙin ba da Isra’ila kawai muke yinsa ba; muna yaƙi da Amurka da Turai da kuma wasu ƙasashen duniya; ya haɗa da duk ababen da ake amfani da su wajen shafe gwagwarmaya da kuma mutanen yankin daga doron ƙasa ta hanyar zalunci da halaka da kuma aikata laifuka."

A watan da ya gabata ne Isra’ila ta kai hare-hare masu yawa a Lebanon kan wuraren da ta yi iƙirarin cewa na Hezbollah ne a wani lamari da ya ta'azzara hare-haren wuce-gona-da-iri da aka shefe shekara ɗaya ana yi tsakanin Isra’ila da kuma ƙungiyar tun lokacin da Isra’ila ta fara yaƙinta na rashin tausayi a Gaza.

Fiye da mutum 2,700 aka kashe kuma kusan mutum 12,500 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra’ila tun watan Oktoban bara, a cewar hukumomin kiwon lafiyar Lebanon. Isra’ila ta faɗaɗa yaƙin ranar ɗaya ga watan Oktoba ta hanyar kai farmaki kudancin Lebanon.

TRT World