Jagoran adawa na Rasha Alexey Navalny 'ya mutu a gidan yari'

Jagoran adawa na Rasha Alexey Navalny 'ya mutu a gidan yari'

Jami'an Rasha sun ce ana bincike kan dalilin mutuwar tasa.
Navalny "ya fara rashin lafiya ne" bayan da ya yi ɗan tattaki a ranar Juma'a, / Hoto: AFP archive

Jagoran adawa na Rasha Alexey Navalny ya mutu, kamar yadda hukumar gidan yari ta yankin Yamalo-Nenets inda ake tsare da shi ta faɗa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Juma'a, hukumar gidan yarin ta gundumar Yamalo-Nenets ta ce Navalny "ya fara rashin lafiya ne" bayan da ya yi ɗan tattaki a ranar Juma'a, "inda nan da nan sai ya fara fita hayyacinsa."

Ta ce daga nan sai aka kira ma'aikatan lafiya, amma sun gaza farfaɗo da Navalny. Ta ce har yanzu ba a gano musabbabin mutuwar tasa ba.

TRT World