Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa biyar a wani hari da suka kai a gabar yammacin kogin Jordan / Hoto: AA

Laraba, 14 ga Agustan, 2024

0930 GMT –– Isra'ila ta kashe mutum 20 a harin da ta kai Zirin Gaza da safiyar Laraba

Akalla Falasdinawa 20 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza.

Mutum bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da Isra'ila ta kai kan wani gida da ke sansanin Nuseirat.

A Khan Younis, Falasdinawa huɗu ne suka mutu a wani harin bam da Isra’ila ta kai kan wani gida inda ta kashe Falasdinawa biyu tare da raunata wasu a garin Bani Suhaila da ke gabashin birnin.

Falasdinawa uku ne suka mutu wasu kuma suka jikkata a wani samame da aka kai a wani gida da ke sansanin Al-Maghazi.

Falasdinawa biyu ne suka mutu wasu kuma suka jikkata sakamakon wani harin bam da aka kai a wani gida da ke yankin aikin Beit Lahia da ke arewacin Gaza.

Har ila yau, an kai hare-hare a yankunan Rafah, Al-Sabra, da Al-Zeitoun a cikin birnin Gaza.

05:34 GMT - Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa biyar a harin da suka kai a gabar yammacin kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa biyar a wani hari ta sama da kuma wani samame da suka kai a arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, in ji majiyoyi daga bangarorin biyu.

Sojojin Isra'ila sun ce ''sun kai hare-hare ta sama kan 'yan ta'adda da dama'' a garin Tammun mai tazarar kilomita biyar daga Tubas.

Gwamnan Tubas Ahmad Saad ya shaida wa AFP cewa an kashe Falasdinawa hudu a Tammun yayin da aka kashe mutum ɗaya a Tubas.

"Sojojin (Isra'ila) sun hana ɗaukar gawar shahidan biyar, kuma a lokacin da muka nemi ofishin hulda da jama'arta an sanar da mu a hukumace game da mutuwar shahidan biyar,'' in ji Saad.

Kamfanin dillancin labarai na Wafa a kasar Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, "dakarun soji sun shiga Tubas da asuba, inda suka harbe wani matashi da ke ɓoye a gidansa."

1330 GMT - Sojojin Isra'ila sun kashe wani mutum a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun kai farmaki garin Tubas da ke yankin arewa maso yammacin Gabar Kogin Jordan, inda suka kashe wani Bafalasɗine bayan sun kewaye gidansa.

Kamfanin dillancin labarai na Falasdinu Wafa ya bayyana mutumin a matsayin Fayez Abu Amer, inda ya bayyana cewa an kashe shi ne bayan tsare shi da sojojin Isra'ila suka yi a ƙawanyar da suka yi wa gidansa.

A cewar wakilin Anadolu, farmakin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a Tubas ya haifar da arangama da Falasdinawan yankin.

Kazalika, sojojin Isra'ila sun kai wani harin samame garin Tamun, inda suka far wa gidaje da dama.

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa wani Bafalasɗine ɗaya ya samu mummunan rauni a harin da aka kai asibitin gwamnati na Tubas.

0554 GMT - Sojan Isra'ila ya kashe wani Bafalasɗine a kusa da Gabashin Kudus

Wani sojan Isra'ila ta harɓe Sheha, mai shekaru 16 a duniya, yayin da yake wankin mota a daren ranar Talata a Anata da ke yankin gabashin Kudus da aka mamaye.

Majiyoyin kasar sun sanar da cewa, wani sojan haramtacciyar kasar Isra'ila da ke cikin da ke zama a Pisgat Ze'ev ne ya kai wa Sheha hari, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Ƙasar Falasdinu Wafa ya bayyana.

0034 GMT - Wakilin Falasdinu a MDD ya bukaci Kwamitin Sulhu ya sanya wa Isra'ila takunkumi

Wakilin Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour ya bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya sanya wa Isra'ila takunkumi a daidai lokacin da take ci gaba da kashe fararen hula a duk fadin Gaza da ta yi wa kawanya.

''Isra'ila na ci gaba da kashe rayukan mutane tare da ɗaukar duk wani mataki da ka iya rura wutar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da muke gudanar da taron cika shekaru 75 na yarjejeniyar Geneva,'' in ji Mansour a wani taron gaggawa na kwamitin sulhu da Aljeriya ta buƙaci a gudanar bayan Isra'ila ta kai wani mumunan hari ta sama a wata makaranta da Falasdinawa ke samun mafaka.

"Bari na fayyace muku hali da ake ciki, Isra'ila ba ta damu da sukar ku ba.. ta yi watsi da kuɗurorinku, ba ta jin muhawar da ku,'' in ji Mansour, yayin da yake nuni kan wakilin Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan.

Da yake kira ga mambobin kwamitin da kar su yi watsi da aikinsu su kuma yi amfani da duk damarmakin da suke da su don aiwatar da matakai, jakadan Falasɗinu ya tambayi cewa: Sai yaushe ne za a kama gwamnatin Isra'ila da laifukan da take aikatawa?

Ya bukaci cewa "lokaci ya yi da za a sanya takunkumi" ga Isra'ilawa da ke da alhakin aikata laifukan yaƙi kuma ya ce: "Yaushe ne za ku aiwatar da shawararku da dokokin kasa da kasa? Kuna buƙatar sanya takunkumi a kan waɗannan masu laifi."

TRT World