Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa adadin yaran da aka kashe a Gabar Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, kuma bai kamata a manta da wahalhalun da suka fuskanta ba.
"Wannan shekarar ita ce mafi muni da yara suka taba fuskata a Gabar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Gabashin Kudus, cikin masifar tashin hankali mai nasaba da rikice-rikice da ya kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba," a cewar Daraktar UNICEF a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka Adele Khodr a ranar Alhamis.
Ta bayyana cewa " an kashe yara 83 a cikin makonni goma sha biyu zuwa yanzu - kusan ninki biyu na adadin yaran da aka kashe a shekarar 2022, a cikin zafafan hare-hare soji da jami'an tsaro."
Khodr ta kara da cewa “fiye da yara 576 ne suka samu raunuka, yayin da rahotanni suka yi nuni da cewa ana tsare da wasu. Kazalika Gabar Yammacin Kogin Jordan ya fuskanci matsi na hana shige da fice.''
"Yayin da duniya ke kallon irin munanan abubuwan da ke faruwa a Gaza, yara a Gabar Yamma da Kogin Jordan suna fuskantar mummunar ukuba, suna rayuwa cikin tsoro da bakin ciki yanayin da a yanzu ya zama ruwan dare,” in ji ta.
"Wahalhalun da kananan yara ke fuskanta a Gabar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Gabashin Kudus, ba za su bace daga zukatansu ba bayan rikicin da ake yi a yanzu - wannan wani abu ne da yake tabbas," a cewar Khodr.