Al'ummar Rafah sun ƙaru zuwa kusan miliyan 1.5, wanda ya ƙunshi dubban mutanen da suka rasa matsugunansu daga Tsakiya da Arewacin Gaza. / Photo: AA

0939 GMT — Isra'ila ta fara hari a Rafah cikin sirri don guje wa "masu martani"

Ma'aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta bayyana cewa, Isra'ila ta fara kai hare-hare a Rafah "ba tare da sanarwa ba, don kauce wa martanin kasashen duniya kuma ba tare da jiran izinin kowa ba".

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta yi Allah wadai da ƙaruwar hare-haren bama-bamai da kuma ɓarna da sojojin Isra'ila suke yi a birnin Rafah, tana mai cewa ta hanyar kai wadannan hare-hare, da gangan Isra'ila ta yi watsi da gargadin da kasashen duniya ke yi kan hadarin kutsawa cikin birnin.

Al'ummar Rafah sun ƙaru zuwa kusan miliyan 1.5, wanda ya ƙunshi dubban mutanen da suka rasa matsugunansu daga Tsakiya da Arewacin Gaza.

1155 GMT — An kashe wani kwamandan sojin Isra’ila a asibitin Al-Shifa

Rundunar Sojin Isra’ila ta sanar da cewa an kashe ɗaya daga cikin kwamandojinta da ke yaƙi a Zirin Gaza.

An kashe kwamandan ne a asibitin Al-Shifa a yayin wani samame da sojojin suka kai asibitin, inda suke zargin akwai mayaƙan Hamas a ciki.

Kafin mutuwarsa, Sebastian Haion mai shekara 51, shi ne kwamandan 401 Armored Brigade. Hakan ya kawo adadin sojin Isra’ila da aka kashe tun bayan soma wannan yaƙin zuwa 594.

0804 GMT — Blinken zai je Saudiyya da Masar domin tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken zai je Saudiyya da Masar a wannan makon domin tattaunawa kan yadda za a tsagaita wuta a rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Gaza, da kuma yadda za a ƙara yawan kayan agajin da ake kaiwa Falasɗinu.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mattew Miller ne ya bayyana haka inda ya ce Blinken ɗin zai tattauna da jagororin Saudiyya a Jeddah a ranar Laraba inda a ranar Alhamis zai wuce birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa da shugabannin Masar.

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza a kullum inda take kashe ɗumbin jama’a akasarinsu yara da mata.

0129 GMT — Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a kan gidaje a Gaza, ta kashe Falasdinawa 20 da ta yi wa ƙawanya

Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun bayyana cewa da sanyin safiyar yau Talata 20 ga wata ne aka kashe Falasdinawa 20 a hare-haren da Isra'ila ta kai a Rafah da wasu yankuna a tsakiyar Gaza.

Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce mutum 14 ne suka mutu kana wasu da dama suka jikkata, sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan gidaje da gidaje da dama a birnin Rafah da ke kudancin Gaza a kusa da kan iyakar Masar, inda Falasdinawa sama da miliyan ɗaya suke samun mafaka,.

Wasu karin mutum shida sun mutu a wani harin da aka kai ta sama a wani gida a sansanin Al-Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, in ji su.

A Deir al Balah, wani gari da ke tsakiyar Gaza mai tazarar kilomita 14 kudu da birnin Gaza, ƙarar fashe-fashe da suka haɗe da tsawa, da ruwan sama sun ƙara jefa iyalan da suka rasa matsugunansu a sansanonin cikin tashin hankali da fargaba.

"Ba za mu iya bambance tsakanin sautin tsawa da tashin bama-bamai ba," in ji Shaban Abdel-Raouf, mahaifin 'ya'ya biyar, ta wata manhajar tattaunawa.

“Mun kasance a da muna jiran damina muna roƙon Allah ya kawo ta da wuri. Amma a yau muna addu’ar kada a yi ruwa, mutanen da suka rasa matsugunansu suna cikin matuƙar wahala,” in ji shi.

2200 GMT —

Trudeau ya bayyana damuwarsa ga Gantz game da shirin mamaye Rafah

Firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya bayyana damuwarsa kan harin da Isra'ila ke shirin kai wa yankin Rafah da ke kudancin Gaza a wata ganawa da ya yi da wani dan majalisar ministocin yakin Isra'ila Benny Gantz.

A wata sanarwa da ofishin Trudeau ya fitar ya ce "Firaministan ya bayyana damuwarsa kan harin da Isra'ila ke shirin kaiwa a kudancin birnin Rafah da ke kudancin Gaza da kuma mummunan tasirin jinƙai ga daukacin fararen-hula da ke fakewa a yankin."

"Ya kuma jaddada bukatar ƙara yawan taimakon jinƙai na ceton rayuka ga fararen-hula da kuma tabbatar da ganin an kai ga duk masu buƙata cikin aminci ba tare da ɓata lokaci ba."

TRT Afrika da abokan hulda