Babu wani martani daga Falasdinu a kan wannan ikirari. / Photo: AFP

1730 GMT — Isra’ila ta karfafa tsaro a Tekun Maliya bayan da aka kai mata harin jirgi marar matuki daga Yemen

Rundunar sojin Isra’ila ta jibge jiragen ruwa ɗauke da makamai masu linzami a Tekun Maliya a matsayin garkuwa, kwana guda bayan da ƙungiyar Houthi mai alaƙa da Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila tare da shan alwashin sake kai wasu a nan gaba.

Ƙungiyar ta Houthi a ranar Talata ta ce ta ƙaddamar da hare-hare uku na jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami a kan Israila tun farkon fara yaƙin nan ranar 7 ga watan Oktoba.

Ta sha alwashin cewa za ta ƙara kai irin waɗannan hare-hare don “taimaka wa nasarar Falasɗinawa.”

Israi’a ta ce ta kare wata barazana ta hari da ake kai mata ta kan Tekun Maliya, sannan Ministan Tsaron ƙasar Adviser Tzachi Hanegbi a ranar Talata ya ce ba za a lamunci hare-haren Houthi ba, amma ya ƙi yin ƙarin bayani a kan yiwuwar mayar da martani.

1603 GMT — An lalata motocin Isra'ila hudu a arewacin Gaza: Hamas

Ƙungiyar Hamas ta sanar da cewa an lalata wasu motocin Isra'ilan huɗu da makamai masu linzami samfurin "Yasin 105" a garin Beit Hanoun a arewcin Gaza.

A sanarwar da ta fitar wacce Anadolu ya samu kwafi, Rundunar Qassam Brigades ta ce mayaƙanta "sun samu damar lalata motoci huɗu da makamaki masu linzami samfurin 'Yasin 105' inda suka kai hari kan wani ƙaramin sansanin soji da ke wani gini a Beit Hanoun.

Ƙungiyar ta kuma ta ƙaddamar da wani hari da jirage marasa matuƙa na Al Zouari a inda sojojin Isra'ila suke a can gefen Gaza, ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.

1555 GMT —Isra’ila ta ce dakarunta na kofofin shiga Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta suna bakin ƙofar shiga Gaza a yayin da ake tsaka da kai wasu gagaruman hare-hare kan yankin na Falasɗinu.

Rundunar dakarunmu ta 162 “suna can cikin Gaza, a bakin ƙofofin shiga birnin,” a cewar kwamandan rundunar Itzik Cohen a wata sanarwa.

“Mun karya lagon Hamas a cikin kwana biyar din da suka wuce sannan mun kai hari muhimmin wajen da take ayyukanta,” ya ce.

Babu wani martani daga Falasdinu a kan wannan ikirari.

Rundunar sojin Isra’ila na faɗaɗa kai hare-harenta ta sama da ta ƙasa a Gaza, wacce take ta fama da haren-haren na Isra’ila tun bayan harin ba-zata da Hamas ta fara kai wa a ranar 7 ga watan Oktoba.

1431 GMT — Sojojin Isra’ila 15 aka kashe a sabuwar gwabzawar da aka yi a Gaza

Sojojin Isra’ila 15 ne aka kashe a jiya da dare a Gaza, inda adadin wadanda aka kashe tun fara yakin zuwa 330 a cewar gidan jaridar kasar.

A ranar Laraba, Gidan Talabijin din isra’ila ya sanar da mutuwar wani sojan kasar bayan kasha wasu tara a gwabzawar da aka yi da dare a Gaza.

Daga baya sai aka kara yin bayani cewa an kashe wasu biyar kuma a gwabzawar, inda adadin wadanda aka kasha tun ranar Talata ya koma zuwa 15.

A wani taron manema labarai a ranar Laraba, Mai Magana da Yawun Sojin Isra’ila Daniel Hagari, ya bayyana cewa kashe sojojin da aka abin bakin ciki ne “matuka”.

1344 GMT — Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza don ɓoye galabar da aka yi a kanta

Shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya zargi Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Gaza domin ta boye galabar da aka samu a kanta.

Isra’ila na aikata mummunan kisan kiyashi kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba’

Ya fadi haka ne a wani sakon bidiyo inda ya kara da cewa “wannan tsagerancin ba zai cece su daga rashin yin nasara ba.”

Ya ce wadanda aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza su ma sun fuskanci “mutuwa da barna” kamar yadda Falasdinawa suka fuskanta.

Hamas ta gaya wa wadanda ke shiga tsakani cewa ya kamata a dakatar da wannan “kisan kiyashin”, kuma ta yi kira da a ci gaba da zanga-zanga musamman a Kasashen Yamma, domin matsa wa hukumomi, in ji Ismail Haniyeh a wani sakon bidiyo

1257 GMT — Italiya na aiki don fitar da ƴan ƙasarta daga Gaza in ji Ministan Harkokin Waje

Ministan Harkokin Wajen Italiya ya ce ƙasarsa tana ƙoƙarin ganin ta fitar da ƴan ƙasarta daga Gaza.

"A safiyar nan aka buɗe kan iyakar Rafah har ma an fara kwashe rukunin farko na mutane. Muna aiki kan yadda ƴan Italiya za su bar Gaza," kamar yadda Antonio Tajani ya sanar a shafinsa na X.

Ya ƙara da cewa ofishin jakadancin Italiya da ke Alkahira ya shirya don karɓar su. Kazalika kamfanin dillancin labarai na ANSA ya rawaito ministan yana cewa yana fatan ƴan Italiya za su iya barin Gaza a ranar Laraba.

1235 GMT — Iran ta bukaci kasashen Musulmi su daina huldar kasuwanci da Isra'ila

Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce akwai bukatar kasashen Musulmi su daina hulda da Isra'ila. Hoto/Reuters

Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bukaci kasashen Musulmi da su daina duk wata hulda ta kasuwanci da Isra’ila, ciki har da cinikin man fetur.

Iran din ta bayyana haka ne sakamakon irin hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Gaza.

“Dole ne gwamnatocin Musulunci su dage kan a daina aikata wadannan laifukan,” kamar yadda Khamenei ya shaida wa taron dalibai a Tehran.

“Kada kasashen Musulmi su rinka hada kai ta fannin tattalin arziki da masu tsatsauran ra’ayin Yahudawa,” in ji shi, inda ya yi kira da a daina kasuwancin man fetur da abinci da su.

1150 GMT — Isra'ila ta sanar da tura jiragen ruwanta na yaki Tekun Bahar Maliya

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da tura jiragen ruwa na yaki zuwa Tekun Bahar Maliya, inda ta ce ta yi hakan ne saboda tsaro.

A shafin X, rundunar sojin Isra’ila ta wallafa hotunan jiragen ruwan nata a Bahar Maliya, wanda tura su na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare cikin Gaza.

0920 GMT — Isra'ila ta sake katsa hanyoyin sadarwa da intanet a Gaza

Isra’ila ta sake katse hanyoyin sadarwa da na intanet baki daya a Zirin Gaza da safiyar Laraba, kamar yadda kamfanin sadarwa na Paltel ya koka.

Kamfanonin da ke sa ido kan intanet na duniya sun tabbatar da sake batun sake katse intanet din a Zirin na Gaza.

A ranar Lahadi ne kamfanin na Paltel ya tabbatar da dawowar sabis din a hankali a Gaza.

0852 GMT — Kasashen duniya sun soma janye jakadunsu daga Isra'ila

Kasar Bolivia a ranar Talata ta ce ta yanke huldar dilfomasiyya tsakaninta da Isra’ila sakamakon irin harin da take kai wa Gaza.

Haka kuma kasashen Colombia da Chile su ma sun yi wa jakadunsu kiranye domin tuntuba.

Duka kasashen sun nemi a tsagaita a yakin da ake yi inda kasashen Mexico da Brazil da ke yankin Latin America su ma suka yi kira kan tsagaita wutar.

TRT Afrika da abokan hulda