1446 GMT — Isra'ila na yi wa dubban Falasɗinawan da ke tsare horon yunwa — Kungiyar Fursunonin Falasɗinu
Wata ƙungiyar Falasdinu ta zargi Isra'ila da yi wa Falasdinawa sama da 9,100 horon yunwa, waɗanda ake tsare da su a gidajen yari.
Wata wata kungiya mai zaman kanta ta Falasdinu ta ce mahukuntan gidan yarin Isra'ila na ci gaba da yi wa fursunoni sama da 9,100 da suka hada da mata da kananan yara da marasa lafiya horon yunwa.
"Isra'ila kuma tana takura musu da hana su 'yancin gudanar da ibadarsu," in ji sanarwar.
"Horon yunwa shi ne mataki mafi hatsari da Isra'ila ke amfani da shi tun bayan mamayar da ta yi wa yankin Gaza ranar 7 ga Oktoba, baya ga azabtarwa da cin zarafi," in ji ƙungiyar fursunonin.
0946 GMT Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 67 a kwana guda
Akalla Falasdinawa 67 ne Isra’ila ta kashe yayin da wasu 106 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a daidai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza da ta yi wa kawanya, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar a yau Litinin, ranar farko ta watan Ramadana.
Wannan ya jawo adadin Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe ya kai 31,112 tare da raunata 72,760 tun bayan soma wannan yaƙin.
Haka kuma ma’aikatar lafiyar lafiya ta sanar da cewa akwai aƙalla mutum 25 da suka rasu sakamakon ƙishirwa da yunwa.
0823 GMT — Isra'ila ta kashe gomman Falasɗinawa a ranar farko ta Azumin Ramadana
An kashe gomman Falasɗinawa an raunata da dama a wani hari da Isra’ila ta kai a Gaza a rana ta farko ta Azumin Ramadana a ranar Litinin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu wato WAFA ya ruwaito.
Rahotanni sun ce jirgin yaƙin Isra’ila ya kashe mutane a dama a unguwannin Zaytoun da Sabra da kuma birnin Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza.
Haka kuma sojojin na Isra’ila sun ƙona wata gona a unguwar Salam wadda ke a birnin Rafah.
0140 GMT — Sarkin Saudiyya ya yi kira kan kawo ƙarshen 'munanan laifukan' da ake yi a Gaza
Sarki Salman na Saudiyya ya yi kira a cikin saƙonsa na watan Ramadan ga ƙasashen duniya da su kawo ƙarshen munanan laifukan da ke faruwa a Gaza, inda Isra'ila ta shafe sama da watanni biyar tana gwabza yaƙi a yankin.
Da yake magana a matsayin mai kula da wurare biyu mafi tsarki na Musulunci, Sarki Salman ya yi godiya kan “yadda aka albarkaci Masarautar Saudiyya”, amma ya ce yaƙin da ake yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya zai sa a yi azumi da sauran ibadu cikin rashin walwala.
“Yayin da muke maraba da shigowar watan Ramadan a wannan shekara,ranmu ya yi matuƙar ɓacin kan yadda ‘yan'uwanmu Falasɗinawa ke ci gaba da fuskantar hare-haren wuce-gona-da-iri,” in ji shi.
"Muna kira ga ƙasashen duniya da su kiyaye nauyin da ke wuyansu na kawo ƙarshen waɗannan munanan laifuka tare da tabbatar da kafa hanyoyin jinƙai da na agaji."
2300 GMT — Sojojin Isra'ila sun gano an harba rokoki 30 daga Lebanon zuwa Tuddan Golan
Gidan rediyon rundunar sojin Isra'ila ya bayyana cewa an harba rokoki 30 daga ƙasar Lebanon zuwa garin Majdal Shams da ke yankin Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye, wanda ya zo daidai da ƙarar jiniya.
Gidan rediyon bai fayyace ko an samu asarar rayuka ba.
Ba a bayar da rahoton ko wasu sun ɗauki alhakin kai harin ba.
A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ta gano mayaƙa ɗauke da makamai masu linzami a yankin gonakin Shebaa da ke kudancin kasar Labanon kuma jiragenta biyu sun kai musu hari kafin su harba makaman.
2100 GMT — Jirgin ruwan Red Crescent na Turkiyya ya isa Masar ɗauke da kayan agaji ga Gaza
Jirgin ruwan Bayar da Agajin Gaggawa na Turkiyya na Bakwai dauke da kayan agaji ga Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya ya isa tashar ruwan El Arish ta Masar.
Kayayyakin agajin da ake bukata za su shiga Gaza ta Masar, a kan iyakar Rafah da ke kudancin kasar.
Jirgin yana ɗauke da kaya sama da ton 2,700 da suka hada da buhunan abinci da ke dauke da shiryayyen abinci da ruwa da fulawa da tufafi da kayan tsafta da kayan matsuguni kamar tanti da jakunkuna da barguna da kayan aikin likita da kayan jarirai.