Ana yawan zargin Isra'ila da keta haƙƙoƙin dan adam a kan Falasɗinawa a sansnain soji da ke Sde Teiman. / Photo: Reuters

Kungiyar kare Falasɗinawa fursɗunoni ta bayyana cewa "bayan shafe kwana 250 Isra'ila na aikata kisan kiyashi, har yanzu mahunkuntanta na ci gaba da kama Falasɗinawa inda ya zuwa yanzu suka kama sama da 9,170 a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da Birnin Ƙudus da wasu dubban daga Gaza."

"Mamayar ta janyo aikata manyan munanan laifuka" kan fursunonin, inda aka samu rasa rayuka aƙalla 18, sannan aka yi hasashen cewa "gomman Falasɗinawan Gaza sun yi shahada", in ji kungiyar a ranar Laraba.

Kungiyar ta ci gaba da cewa "Wannan mamaya a baya-bayan nan ta janyo shahadar ɗaurarru 36 daga Gaza, kuma har zuwa yau, Isra'ila ta ƙi bayyana su waye suka mutu, kuma a wane yanayi."

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da cewar an kama mata 310 da ƙananan yara aƙalla 640.

Idan har hakan ta tabbata, "Adadin 'yan jarida da aka kama sun kai 85, inda 52 suke tsare har yanzu, cikinsu har da 'yan jarida 14 daga Gaza."

"Daga cikin wadanda aka tsare akwai mata 'yan jarida shida bisa zargin su da Isra'ila ke yi da tunzura jama'a."

Sun kuma yi tsokaci da cewar adadin waɗanda aka kama bisa zarge-zarge ya kai kusan mutum 6,627.

Kama mutane da Isra'ila ke yi ta wannan hanya ya munana, inda take azabtar da Falasɗinawa, kuma takan ɗaure su har tsawon watanni shida.

Ƙungiyar sanya idanu kan fursunonin ta kuma ce "Batun tsare mutane a Gaza babban ƙalubalen ƙungiyoyin kare hakkokin ɗan'adam a yanzu, musamman yadda ake ci gaba da samun ɓatan Falasɗinawa, kuma suna hana ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su ziyarci inda wadanda suka kama ɗin suke domin duba yanayin da suke ciki."

Azabtarwa da cutarwa

Dangane da azabtar da waɗanda aka kama, ƙungiyar ta ce "hanyoyin azabtarwa sun haɗa da hana ruwan sha da yunwa da hana muhimman abubuwan da ɗan'adam ke buƙata."

Ta ƙara da cewa "Yaɗuwar cututtukan fata a tsakanin waɗanda aka tsare, musamman ƙarzuwa, saboda rashin tsafta, musamman yadda mahukuntan gidajen yarin suka hana sauya kaya, kowa tufafi ɗaya gare shi. Sannan suna cunkusa mutane a wajen."

Ƙungiyar kare muradun fursunonin ta yi kira da a "gudanar da binciken ƙasa da ƙasa kan zalunci da muzantawar da ake yi wa wadanda aka kama aka tsare a yankunan da aka mamaye."

Wani bincike na baya-bayan nan ya bayyana yadda Isra'ila ke take haƙƙoƙin ɗan'adam a wani sansanin soji a Sde Telman da ke kudancin Isra'ila.

Sauran hanyoyin azabtarwa da suka wuce a iya bayaninsu sun haɗa da zura karfe a duburar mutane, da jona wa mutum lantarki, da kuma duka da ƙarafa da bayan bindiga.

Yaƙin kisan kiyashi

Isra'ila ta yi kutse da mamaya a Gaza tun bayan da Hamas ta kai hari a ranar 7 ga Oktoba kan sansanin sojinta da a baya ƙauye da gonakin Larabawa ne.

Hamas ta bayyana cewar ta kai harin na ba-zata kan maƙiyarta don mayar da martani ga hare-hare kan Masallacin Ƙudus, da cin zarafin da 'yan kama guri zauna a Yammacin Gabar Kogin Jordan da kuma dawo da batun Falasɗinu kan teburin tattaunawa.

Mayaƙan na Hamas sun nufi wurare 22 a wajen gaza, ciki har da garuruwa da unguwanni da ke da nisan kilomita 24 daga katangar Gaza.

A wasu wuraren, an ce sun kashe sojoji da dama na Isra'ila inda ita kuma ta fara mayar da martani. A musayar wutar da aka yi an kashe sama da mutane 1,130, kamar yadda jami'an Isra'ila da kafafan yaɗa labaran yankin suka sanar.

Mayaƙan Falasɗinawa sun kama sama da fursunoni 250 inda a yanzu suke tsare da 116 a Gaza, ciki har da 41 da sojojin Isra'ila suka ce sun mutu, wasun su sun mutu a hare-haren kan mai uwa da wabi na Isra'ila.

Tun bayan fara kisan kiyashi a Gaza, Isra'ila ta kashe akalla Falasɗinawa 543 da jikkata kusan 5,200 a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan, kamar yadda alƙaluman Ma'aikatar Lafiya suka bayyana.

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 37,202 - kashi 71 mata ne da yara kanana - ta jikkata 84,932 inda aka yi amanna da an binne sama da 10,000 a ƙarƙashin gine-ginen da ta yi wa ruwan bama-bamai.

Mahukuntan Isra'ila ne ke da alhakin "laifukan yaƙi da keta haƙƙoƙin ɗan'adam" a yayin kai hare-hare Gaza tun 7 ga Oktoban 2023, kamar yadda rahoton kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana.

Kwamitin Bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa ya lura da cewa "An dinga kai hare-hare da aka tsara kan fararen hula a Gaza, kuma an dinga azabtar da su da yunwa da rashin kayan more rayuwa."

Falasɗinawa na fuskantar yunwa saboda Isra'ila ta rufe dukkan hanyoyin isa ga yankunan Falasɗinawan, inda ba a iya kai abinci da magungunan da sauran kayan more rayuwa zuwa Gaza da ke da mutum miliyan 2.4.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza.

TRT World